Rundinar ‘yan sanda reshen jihar Kaduna ta samu nasaran aika wasu miyagun ‘yan ta’adda 4 masu garkuwa da mutane zuwa garin da ba’a dawowa.
Kakakin ‘yan sandan jihar Kaduna DSP Muhammad Jalige ya shaida wa manema labarai cewa an jima ana bibiyar ‘yan ta’addan, an datse su akan hanyar Saminaka zuwa Jos suna tafiya a cikin mota kirar Sharon blue colour direban motar mai suna James Dawi, dan shekara 31 wanda ya fito daga garin Vom karamar hukumar Jos South jihar Plateau.
Lokacin da ‘yan ta’addan suka lura ‘yan sanda na bin diddiginsu akan hanyar Saminaka zuwa Jos, sai suka bude wa ‘yan sandan wuta, a gurin musayen wuta na tsawon mintuna 30 ‘yan sanda suka samu nasaran aika ‘yan ta’addan zuwa garin da ba’a dawowa.