Tsohuwar jarumar masana’antar shirya fina finan hausa ta Kannywood Safara’u tasaki wani faifan bidiyonta a Hotel tana tikar rawa.
Safara’u dai ta bayyana cewar ita yanzu ba jarumar Kannywood bace yanzu takoma sana’ar waka a cewarta inda a wakarta tafarko take fadin cewar ita yanzu tabar sana’ar yan wahala.
Saidai duk da irin sukar da jarumar take samu hakan bai hanata janyewa daga kudirinta na zama mawakiyar hip hop ba, takuma bayyana cewar sana’ar waka yanzu tafara gamasu zaginta kuma ita bata damu da hakan ba, sabida daukakace takesa a zagi mutum.
Anan kuma wani faifan bidiyon Safara’u ne tareda mawaki Mr-442 awani Hotel inda take chashewa ita da maigidanta a harkar waka wato Mr-442.