Wata matashiya da ke kaduna ta yi alฦawari har ga Allah, zata saida duk abinda ta mallaka, daga ciki harda iphone ษinta domin saya wa Zulum fom ษin takarar Shugaban ฦasa idan har aka tsaida shi a matsayin ษan takara, Zuma Times Hausa ta rawaito cewa, matashiyar mai suna Zainab Abubakar Bako ta bayyana cewa, “ina miฦa roฦona ga mai girma gwamnan jihar Borno Babagana Umaru Zulum, da ya taimaka ya fito takarar shugabancin ฦasar nan, saboda inada yaฦinin shi zai ฦwato ฦasar nan daga irin ฦangi na matsalar tsaron da muke ciki a yanzu insha-Allah”,
Najeriya tana buฦatar shugaba nagartacce jajirtacce mara tsoro kamar Gwamna Zulum, wanda ya fifita damuwar talakawa da ya ke shugabanta fiye da tasa damuwar”,
“sannan ina kara kira ga shugaban jam’iyar APC Na ฦasa dama dukkan wasu masu ruwa da tsaki a jam’iyar, da su duba wannan kiranye da lissafi, hasashe na siyasa, domin muga Gwamnan jihar Borno an bashi takarar shugabancin ฦasar nan a zaษen 2023, duba da har ya zuwa yanzu Gwamnan bai sai fom na tsayawa takara a jiharsa”,.