tsohuwar jarumar kannywood maijidda ibrahim wacce take waran dangidan ado bayaro tace 'ya 'yan adao bayaro suna neman kasheta haka kawai.

Tsohuwar Jarumar Kannywood wood, Maijidda Ibrahim, matar Alhaji Bello Ado Bayero, Dandarman Kano ta bayyana irin tashin hankalin da ta ke fuskanta a rayuwar aurenta.

Kamar yadda ta bayyana a wani bidiyo da shafin Kannywood ya nuna, ba ta samun matsala da mijinta uban ‘ya’yanta guda 6, 4 maza, biyu mata, sai danginsa su ma mata.

Kamar yadda ta bayyana akwai yayyin mijinta mata da su kr yunkurin ganin bayanta ta hanyar lakada mata duka tare da sheganta mata yaranta.

Ta ci gaba da bayyana cewa duk da shekaru 21 da ta yi a gidan mijinta, har yau su na kiranta karuwa, ‘yar iska, ragowar Kannywood, ‘yar talakawa da sauransu.

Kamar yadda ta bayyana akwai yayyin mijinta mata da su kr yunkurin ganin bayanta ta hanyar lakada mata duka tare da sheganta mata yaranta.

Ta ci gaba da bayyana cewa duk da shekaru 21 da ta yi a gidan mijinta, har yau su na kiranta karuwa, ‘yar iska, ragowar Kannywood, ‘yar talakawa da sauransu.

Babban abin da ya fi ci mata tuwo a kwarya shi ne yadda a kullum su ke sheganta mata yaranta. Ita da mijinta sun kai su kara ga kwamishinan ‘yan sanda amma sun ki amsa gayyatar da aka yi musu.

Ta ce har sarki sai da ya yi musu sulhu tsakaninsu amma aban ya ci tura don ko da sallar nan da ta gabata sai da su ka dake ta har da cizge mata gashin kanta.

A cewarta, don ta kafa shaida ne ya sa ta fito fili ta ke bayyana wa duniya saboda ba ta san me gobe za ta haifar ba.

Ta bukaci taimako daga jama’a kasancewar kullum a cikin fargaba ta ke kada hakan ya sanya wa mijinta damuwa ko kuma ya yi ajalinsa.

Ta bayyana sunayensu, inda ta ce akwai Rabi wacce ake ce wa Rabin Daura, sirikar Bashar Mai Daura sai Kuma Hauwa Lele, wacce Madakin Kano ya taba aure, su ne su ka saka ta a gaba.

Ta bayyana yadda Rabi da Hauwa Lele su ka taba zuwa har gidanta su ka yi mata dukan tsiya.

Ta bayyana yadda bayan Hawan Pamisau ya je gaishe da Sarki, daga nan su ka gayyaceta zuwa wani daki su ka fara zarginta.

Bayan ta nemi ramawa ne su ka taru suka dinga dukanta har da yaga mat sutturar da je jikinta da kuma cizge mata gashin kanta.

Anan ta shiga mawucayacin yanayi. Ta bayyana cewa ba sa kaunarta ko kadan, akwai manyan da ke sonta amma kananun dai iyakar tsana suna nuna mata.

Post a Comment

Previous Post Next Post