innalillh auran ummi rahab da lilin baba yanasamun tan garda sabida wasu dalilai ๐Ÿ‘‡

Idan bazu mantaba kasa da wata biyu kenan muka sanar muku irin soyayyar dake tsakanin jaruma Ummi Rahab da mawaki Lilin Baba inda zamuce wannan soyayya tasamo asaline tun bayan rikicin ummi rahab da jarumi Adam a zango.

Inda mawakin da budurwar tasa sun daidaita kansu inda Tashar TsakarGida ta rawaito cewar ana shirye shiryen Auren mawaki Lilin baba da Ummi Rahab bayan karamar sallah shekarar 2022.

Saidai makonni biyu kenan sa wasu alamura marasa dadi suka bayyana, inda wani faifan bidiyon Ummi Rahab yayita yawo a kafofin sada zumunta inda bidiyon an dauki Ummi Rahab bata sani ba tana sanye da riga vest irin wacce mata kan sakawa idan suna zaune acikin gidansu kokuma gidan mazajensu.

Saidai wasu rahotanni sun bayyana cewar akwai wanda suke son bata auren jaruma Ummi Rahab shiyasa suka saki wannan bidiyon domin su zubar mata da mutunci dakuma lalata shirin aurenta da masoyinta.

Mufeedah rasheed wata mai tsokaci a dandalin sada zumunta na Instagram tafito ta koka kan yadda wasu suke hada tuggu da munafurci kan lallai saisun wargaza auren Ummi Rahab da masoyinta Lilin Baba. Gadai abinda Mufeedah ta rubuta a shafinta na Instagram

Post a Comment

Previous Post Next Post