Ya ce Buhari ya gaza matuฦa ta fannoni da dama, musamman wajen kasa samar da ingantaccen shugabanci ga ‘yan Najeriya.
Ya ce a yanzu Najeriya a ruษe ta ke, kuma a gigice al’ummar ฦasar su ke, saboda Buhari ba shi ma da kuzarin da zai iya tashi ya nuna shi shugaba ne mai iya yi, ko mai iya sawa a yi ko ya ce a bari, kuma a
Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi, kuma ษan takarar shugaban ฦasa na zaษen 2023 a ฦarฦashin PDP, ya ragargaji gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, inda ya ce “maฦaryata da ‘yan-amshin-Shata ne kewaye da Buhari, shi ya sa bai samar da sauฦin da ya riฦa zuguguta cewa zai samar a Najeriya ba.”
Bala Mohammed ya bayyana haka ne a lokacin da ya dira Katsina wurin taron ganawa da wakilan zaษen ‘yan takara, a ranar Lahadi.
Ya ce Buhari ya gaza matuฦa ta fannoni da dama, musamman wajen kasa samar da ingantaccen shugabanci ga ‘yan Najeriya.
Ya ce a yanzu Najeriya a ruษe ta ke, kuma a gigice al’ummar ฦasar su ke, saboda Buhari ba shi ma da kuzarin da zai iya tashi ya nuna shi shugaba ne mai iya yi, ko mai iya sawa a yi ko ya ce a bari, kuma a bari.
“Jihar Katsina na da tarihin samar da shugabanni nagari. Mun ga abin da marigayi Umaru Musa ‘Yar’Adua ya yi a zamanin sa. Amma shi Buhari bai kewaye kan sa mutanen da su ka cancanta ba, sai ya tattago gungun maฦaryata da ‘yan-amshin-Shata su ka kewaye shi.
“
A kullum su na shirya masa ฦarairayi. Kuma kun san yadda soja ya ke. Bai san irin tuggu da kitimirmirar mutane ba, kuma bai san yadda gwamnati ke aiki ba. Bai san yadda ake tafiyar da gwamnati ba
Buhari ba ya shiga karkara cikin talakawa. Sai dai ya yi zaune a Fadar Shugaban ฦasa, maฦaryata na kai masa ฦarairayi, shi kuma ya na yarda da duk abin da su sanar da shi.”.