Rahotanni daga jihar Kano a arewa maso yammacin Najeriya na cewa bam ya tashi a Aba Road da ke Unguwar Sabon Gari a birnin Kanon.
Shugaban Kasuwar Sabon Gari Nafi'u Nuhu Indabo ya tabbatar wa da BBC lamarin, inda ya ce lamarin ya rutsa da mutane da dama ciki har da yara Ζ΄an makaranta.
Wakilinmu da Kano Khalifa Dokaji ya je wajen da abin ya faru, wato makarantar Winner Kids Academy da ake zargin a can aka ta da bam din.
"Rufin makarantar ya yaye saboda Ζarfin bam Ιin. Dukkan hanyoyin da suke kusa da wajen sun cika maΖil da jama'a waΙanda ke ciki da damuwa da alhini," in ji Dokaji.
Tuni kwamishinan Ζ΄an sanda na jihar Kano CP Sama'ila Dikko da shugaban hukumar DSS na jihar sun halarci wajen, sannan motocin asibiti sun je don kwasar waΙanda harin ya rutsa da su.
Hukumomi ba su kai ga fadin adadin wadanda abin ya rutsa da su ba, amma Khalifa Dokaji ya ce ana iya ganin jini ta ko ina a wajen da kuma wasu sassan jikin mutane.
Jami'an tsaro sun yi ta ΖoΖarin shawo kan mutane waΙanda da alama ke fusace, don su bari a yi bincike kan musabbabin faruwar lamarin.
An daΙe ba a ji labari mai kama da wannan ba wato na kai harin bam a jihar Kanon, dalilin da ya sa hakan zai jefa mutane cikin ruΙanin wa yake da alhakin hakan.
Ba a Kano kaΙai ba, an samu sauΖin tashin bam a faΙin Najeriya a shekarun bayan nan, ba kamar a da ba da hakan ya zama kusan ruwan dare.
Za mu ci gaba da kawo muku Ζarin bayani kan labarin, sai ku dinga sabunta wannan shafi.