Zakatul Fitr Yadda Ake Zakkar Fid da Kai

Malamin addinin Musulunci a Najeriya, Dr Jabir Maihula, ya yi bayani dalla-dalla kan yadda ake Zakkar Fid-da-kai kwanaki kadan kafin gudanar da karamar Sallah.

Malamin ya bayyana tasirin da Zakkar Fid-da-kai ke yi a tsakanin Musulmi:

  • Tabbatar da wadatar abinci tsakanin musulmai, ko wanne musulmi ya yi sallah da abincin da zai ci da iyalinsa.
  • Ana amfani da Zakkar Fidda-kai wajen kankare zunuban da musulmi ya aikata cikin azumi, wadanda ba su ɓata masa azuminsa ba amma sun rage masa lada.
  • Tana kara zumunci da soyayyar juna tsakanin musulamai.

Yadda ake fitar da ita

Dr Jabir Maihula ya ce ana fitar da Zakkar da dukkan wani nau'in abinci da al'ummar da mutum ke rayuwa cikinta ke ci, musamman tsaka-tsakin abincin da aka fi ci, ko kuma abincin da suka fi ci gwargwadon hali.

Malamin ya ce an fi son abin da mutum yake ci ya fitar da zakkar da shi, amma ba "wajibi ba ne don mutum yana cin shinkafa a gidansa ace sai ya yi zakkar da ita.

Wadanda ya kamata su fitar da ita

Idan mutum yana da wadata zai fitar wa kansa ya kuma fitar wa da wadanda ke karkashinsa wato mutanen da yake ciyar da su.

Zakkar tana kan dukkan Musulmin da ya wadatu, wadata ta bangaren abincin da za a ci da kuma wadata ta bangaren kudaden da zai iya bayarwa a sai abincin da su.

Tana kan dukkan musulmi, babu mace babu namiji, babu babba babu yaro, ana fitar wa ga yaran da suke da kudi.

Wasu yaran marayu ne ana iya fitar musu cikin duniyarsu, wasu kuma irin kyautar da ake musu ko kuma wadanda iyayensu ke buɗe musu asusun banki, duk za a fidda zakar cikin kudinsu.

Idan 'ya'yan mutum maza sun balaga kuma lafiyarsu kalau to zakkarsu ta sauka daga kan mahaifansu. Amma idan ya ce zai ci gaba da fitar musu duk da haka, to babu laifi a Musulunce.

Idan kuma mata ne 'ya'yan mutum ko sun balaga zai ci gaba da fitar musu har sai sun yi aure sun yi tarayya da mazajensu, a lokacin ne zakkar take sauka daga kan mahaifinsu.

Post a Comment

Previous Post Next Post