Rahotanni sun ce babbar jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ta hana wa biyu daga cikin 'yan takarar shugaban kasa 17 a zaben 2023 yin takara ฦarฦashin jam’iyyar.
da ta ruwaito labarin ta ce shugaban kwamitin tantance ฦดan takarar David Mark, bai bayyana sunayen waษanda aka hana wa yin takarar ba da kuma dalilin rashin cancantarsu.
Daga cikin ฦดan takarar da aka tantance a ranar Juma’a a hedikwatar jam’iyyar a Abuja sun ฦunshi tsohon mataimakin shugaban ฦasa Alhaji Atiku Abubakar da tsohon shugaban Majalisar dattawa kuma tsohon gwamnan Kwara Sanata Bukola Saraki da gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da gwamnan Bauchi Bala Muhammad da Peter Obi da Pius Anyim