Indiyawa na rayuwa cikin zafi da ya addabi miliyoyi

Miliyoyin Indiyawa na fuskantar tsananin zafi da ya dimauta tare da sanya mutane shiga matsanancin hali. Dabbobi ma ba a bar su a baya ba wajen fuskantar wannan matsala, kuma sam babu alamun sassautawa.

"Zafin yana karuwa a kowacce dakika a kasar, lokacin bazara ya zo cikin sauri," in ji Firaminista Narendra Modi lokacin ganawa da ministocinsa a ranar Laraba.

Hukumar kula da yanayi ta Indiya ta yi hasashen yanayin ka iya kaiwa maki 1-4 a ma'aunin selshiyos a wasu sassan arewa maso gabashin kasar da tsakiyar Indiya cikin wannan makon, ba kuma lallai hakan ya sauya ba.

Duk da kasar ta saba da tsananin zafi, musamman tsakanin watan Mayu da Yuni, bana lokacin ya yi saurin zuwa inda aka fara fuskantar zafin tun farkon watan Maris - yanayin da ba a taba fuskanta ba cikin shekara 122.


Cibiyar kimiyya da muhalli ta ce tsananin zafin na bana ya shafi jihohi 15, ciki har da arewacin jihar Himachal Pradesh, wadda a baya take da yanayi mai sanyi.

Cikin makon nan, ana sa ran zafin zai kai sama da 40 a ma'aunin selshiyos a babban birnin kasar Delhi.

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

Bayanan hoto,

Wata Damusa a gidan ajiye dabbobi ta shiga ruwa domin samun sassauci

Naresh Kumar, babban jami'in kimiyya ne da ke aiki da hukumar kula da yanayi, ya dora alhakin tsananin zafin kan masana'antun da suka karu suke haddasa tsananin zafin.


Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus


Wata babbar matsalar ita ce hankoron da tekun Mediterranean ke yi, hakan na nufin arewa masu gabashin Indiya da tsakiya za su dinga samun zubar ruwan sama kadan. Har wa yau bushewar kasa na kara taka rawa wajen kambama zafin da ake fama da shi, an ga hakan a farkon watan Maris.

Illar da zafin ke yi kusan a bayyane suke. Manoma sun ce shigowar zafin katsaham ya janyo lalacewar amfanin gonar da ba su girbe ba, hakan ka iya janyo matsalar abinci a duniya baya ga yakin da ake yi a Ukraine.

Tsananin zafin ya kara bukatar wutar lantarki, lamarin da ke darsa fargaba a wasu jihohin da ta yiwu makamashin kwal ya yi karanci.

Mr Modi ya yi gargadin akwai hadarin tashin gobara saboda zafi, don haka jama'a su kiyaye.

Dama can, lokacin bazara wani yanayi ne mai tsauri ga wasu sassan da yankunan Indiya. Tun kafin zuwa na'urar sanyaya wuri, da manyan sundukan sanya abu mai sanyi da miliyoyin mutane ke amfani da su, Indiyawa su na da hanyoyin da matakan kariya idan lokacin ya zo, su na adana ruwa a manyan tuluna, da shafa danyan mangwaro a jikinsu domin magance zafi.

Sai dai, yawancin kwararru sun ce a yanzu Indiya na fama da matsanancin zafin da aka dade ba a gani ba, kuma za a dauki lokaci ana yi.

Roxy Mathew Koll, kwarare kan kimiyyar sauyin yanayi a cibiyar kula da yanayi ta kasr, ya amince masana'antun da ake da su cikin gari sun kara matsalar zafin. Sai dai ya kara da cewa ana fama da dumamar yanayi a duniya.

"Wannan shi ne musabbabin karuwar tsananin zafin," in ji shi, ya kara da cewa ana bukatar karin bincike domin alakanta sauyin yanayi da tsananin zafi.

D Sivananda Pai, darakta ne a cibiyar nazari kan sauyin yanayi, kuma ya yi bayani kan karin kalubalen da zafin ke haddasawa masu alaka da sauyin yanayi, misali karuwar al'umma.

Wannan na kara matsalar, da kona dazuka da karuwar a baben sufuri.

"Idan kana da lafiyayyun hanyoyi da gine-gine, an yi wa zafi kofar rago, dan haka zai fara kokarin fita ta hanyar mamaye sararin samnaiya. Wannan ke kara matsanancin zafin," in ji Mr Pai.

Ya ce matsananncin zafin ya fi damun iyalai matalauta.

"Matalauta ba su da hanyoyin sanyaya wuri kuma zabin da suke da shi daya ne; su zauna a gida, su kauce wa fitowa waje," in ji Dr Chandni Singh, babban mai bincike kuma marubucin wani littafi kan sauyin yanayi.

Yayin da aka mayar da hankali kan mace-macen da ake fuskanta sakamakon sauyin yanayi, Mr Singh ya ce masu yin dokoki ya kamata su mayar da hankali kan yadda za a magance matsanancin zafin da ake fama da shi da yadda yake shafar al'umma.

"Tsananin zafi babbar illa ce ga lafiyar bil'adama. Idan zafin ya yi tsanani da dare, jikin dan Adam ba ya samun nutsuwa. Akwai kuma fargabar karuwar kamuwa da wasu cutuka da kashe makudan kudade," in ji shi.

"Akwai wurare da dama a Indiya da ba sa fuskantar zafin, amma idan aka hada da zafin da dumamar yanayi ke haddasawa , lamarin babu sauki. Ya na da kyau masana kimiyya su kara lalubo hanyoyin da matakan da ya a dauka a irin wannan lokacin."

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

Bayanan hoto,

Yawancin Indiyawa ba su da zabi, dole su gudanar da harkokinsu komai zafi

"Yawancin yara a yankunan karkara, suna zuwa makarantun da aka yi su da rufin kwano, ko karkashin inuwar bishiya, lallai zafi zai addabe su," in ji shi.

Tun shekarar 2015, gwamnatin tarayya da ta jihohi sun fitar da sanarwa kan matakan da za a dauka saboda matsanancin zafi, kamar hana ayyuka cikin rana da kuma waje musamman da rana, da shawarwarin yadda ya kamata mutane su kare kansu.

Sai dai hakan za samu ne idan aka ga gagarumin sauyi daga gwamnati ta hanyar garanbawul ga dokokin kwadago, da kara shuka tsirrai a birane, in ji Mr Singh.

"An yi gine-ginenmu da tsarin da suke zukar matsanancin zafi tare da aika shi cikin gidaje, babu kuma hanyoyin shan iska sosai. Ana bukatar yin sauye-sauye matukar da gaske ake yi don saukaka wa mutane zafi."

"Akwai abubuwan da muke yi daidai, amma yawancin lokaci ba daidai muke yi ba, saboda dole dai mu rayu da zafin nan."

Post a Comment

Previous Post Next Post