[www.nairaside.com.ng] Yakson: *YA ZA'AI KA GANE CEWA FARASHIN ZAIYI SAMA๐ NE KO KASA ZAI SAUKA?๐*
To ana iya gane kasuwar Forex ne ta hanyar *Analysis*
Analysis shine kashin bayan Kasuwar Forex Trading, tinda analysis shi ke juya dukkan nin kasuwar.
Analysis Kuma ya kasu, Kashi Uku, sune Kamar haka:-
-Technical Analysis
-Fundamental Analysis
-Sentiment analysis.
Idan muka dauke su daya bayan daya, zaku gane ko wanne amfanin shi, da Kuma matsayar shi a wannan kasuwa ta Forex.
*Technical analysis:-* shi wannan analysis ne da akeyin shi, ta Hanyar karantar Candles na market ko Kuma wasu Halayya da Kasuwa takeyi, nan ne mutum zai fahimci cewa ga inda kasuwa zata nufa, a takaice dai Shi Technical Analysis, kawai analysis ne da akeyin shi ta Hanyar karantar Candles๐.
*Fundamental analysis:-* shi Kuma wannan analysis ne da yake tafiya da labarai ko Kuma wani abu dake faruwa a duniya, idan baku manta ba, na fada muku ita Kasuwar Forex, kasuwa ce ta Duniya, Kuma Babbar kasuwa Wanda ake hada hada ta kudaden๐ธ Duniya, fiye da 5.6Trillion Dollars๐ฐ, sannan wannan kasuwa Bata da wani lkci da za'ace Wai an rufe ta gaba daya, kasuwa ce da zata cigaba daci, har abada....
To shi Technical Analysis duk wani abu dake faruwa a duniya Yana iya juya kasuwar, Misali:- kamar ace yau America, ko England suna zabe (Votes) to zaka tarar a Lokacin *"Dollars ko Pound"* yayi rauni sabida an fito da kudade sabida zabe, Kamar yadda dai ake a Nigeria xakuga Lokacin zabe, an fito da kudi, ya yawaita a gari, to Kamar Haka ne.
Lokacin mu Kuma Traders xamuyi ta siyar da wannan *"Dollars"* din ko *"Pound"*
Wani misalin akwai Lokacin da America ta kaiwa wani Shugaba na Iraq Hari, har ta Kashe shi, to Lokacin sai *Dollar* ta ringa hawa sama sosai...
Yanzu da ace *Donald Trump's* zaije Twitter yai wani Tweet din, hakan sai kuga ya tashi *Dollar* sama ko Kuma ta karye sosai.
Anan dai abinda nakeso ku gane da *Fundamental analysis* shi News ne yake tapiya dashi, sannan Yana da karfin da in yazo Koda kayi *Technical Analysis* fundamental Yana zuwa zai karyama wannan analysis naka.
Anan dai Fundamental Yana da karfi, fiye da ko wane analysis.
*Sentimental analysis:-* shi Kuma wannan Yana tsakanin Technical ne da Fundamental, kawai shi abinda *Sentimental analysis* Kamar competition ne market tana rinjaye ne da adadin Wanda sukafi yawa a market din.
Daman dai na fada muku Major mutanen da suke juya kasuwar Forex sune, Bank, Industries, University da dadai sauran manyan Comfanoni na Duniya.
So shi sentimental kawai zaka duba a Lokacin Buyers ne ko Sellers ne sukafi yawa akan pairs din da zakai Trading to duk Wanda sukafi yawa, sune ake da yaqinin zasu rinjayi Price n market din, Lokacin da Buyers Suka fi yawa tofa Lokacin kasuwar *BUY* zatai tayi, Haka ma idan Sellers ne sukafi yawa a market din to, price n market din *SELL* za'ai tayi.
*Wannan shine bayani akan Forex.
Wanda wanna website mai suna www.nairaside.com.ng ya dauki nawin kawo muku.
Wa da kuma ni yakubu abdulhamid nayi muku rubutun zube
Tags:
FOREX