wasu ababan Al ajabi dangane da maniyin na miji wayanda ma'aurata Basu saniba bare marasa aure

Matan aure da ma wadanda basu taba aurenba, da mazan aure da gwagware, ba dukkaninsu ne suke da masaniya akan irin abubuwan al’ajabi da sinadarin da ake halittar mutum yake da shi ba.
Akasarin mutane abunda suka fi sani kawai shine da zaran maniyi ya shiga mace shi kenan sai ciki.
Ga waau abubuwan da suka kamata duk wasu ma’aurata su sani game da maniyin Namiji.

1_: Ba kamar yadda wasu matan suke dauka ba. Maniyin na miji yana saurin mutuwa da zaran ya shiga cikin mace. Wannan ba gaskiya bane.
Maniyin na miji zai iya yin kwanaki biyar a raye a jikin mace. Don haka duk wata macen aure data yi Jima’in da bana neman haihuwa ba kuma babu wani kariya, ta kwana da sanin cikin zai iya shiga bayan kwanaki 5 Idan bata sha wani magani ba.
Don haka duk Jima’i da aka yi kasa da kwanaki 5 mace na iya yin ciki.
2: Yana da kyau matan aure su fahimci cewa abincin da namiji zai ci ko yake ci dandanonsa da yanayinsa na bayyana a maniyin namiji.
Ga matan da suke tsotso ko wasa da gaban mazansu, yanada kyau ki fahimci abunda kika ciyar da mijinki shine zaki samu a cikin maniyinsa.

Idan kika bashi abinci mai wari, irin tafarnuwa, ko karni irin kifi wannan warin zai bayyana a cikin maniyinsa haka ma abunda ya sha a wanni kadan kamin suma Jima’i.
3: Ba duk mata bane suke da masaniyar cewa maniyi daban, ruwan maniyi kuma daban.
Shi maniyi shine ruwan da namiji yake kawowa a lokacin da yayi zuwan kai. Shi kuma ruwan maniyi shine halittan dake sulalawa ya shiga mahaifar mace wanda shike sata samun ciki.
Wannan yasa masana sukace namiji zai iya kawowa amma ba lalle bane kuma a iya yiwa matarsa ciki idan shi wannan ruwan maniyin nasa yanada matsala.

4: Ma’aurata da dama suna samun matsala wasu lokutan akan lamarin azalu.
Azalu shine cire azzakarin namiji a lokacin da zai yi zuwan kai daga gaban matarsa domin hana maniyi shiga mahaifarta.
Ana samun wani lokacin namiji yana azzalu amma kuma sai matarsa tayi ciki. Wasu mazan sai suna ganin kodai macen tasu tana munafurtarsu ne ko kuma Yaya. Ganin yadda suke zare gabansu daga farjin mace a yayin zuwan kai.
Abunda akasarin maza da mata basu sani ba shine, ba sai namiji yayi zuwan kai bane maniyi yake fita daga gabansa ba. A lokacinda namiji yake saduwa da matarsa ruwan maniyi daga gabansa na iya fita zuwa cikin mace kamin yayi zuwan kai ko kuma daf da zai yi zuwan kai a lokacinda yake kokarin zare gabansa.

Tuni maniyi ya wuce kamin ma ka fidda gabanka daga gaban matarka. Wannan kuma zai iya sa ta samu ciki a lokacinda ka kake ganin kana azzalu.
5: Bayan samar da karin jin dadi ga mace. Yawan maniyi a tare da Namiji yakan bashi damar yiwa mace ciki akan lokaci.
Mafi yawan mata suna son ji namiji ya kawo a cikin gabansu. Akwai matan da muddin namiji zai kawo a wajensu ba zasu taba jin dadin Jima’i ba.
Bawai kawai kawowan ba, mace tana son taji ruwan maniyi ya cika mata mara har yana kwarara. Wannan, bayaga Samar da karin jin dadi na Jima’i, nan da nan mace ke iya samun ciki.
Maniyin Namiji a lokacin da akayi zuwan kai ba kai tsaye suke wucewa cikin mahaifa ba. Hakan yasa dayawa daga cikinsu suke mutuwa a hanyar zuwa mahaifa, amma idan namiji na tsirtoshi dayawa, akwai tsammanin matarsa zata samu ciki da wuri.
6: Mazan da basa yawan yin zuwan kai suna samun matsalar ciwon mara akai akai da kuma rashin karfin kuma lafiyayyen maniyi.
Masana sukace a lokacinda maniyi ya taro a mataran namiji bai samu fita ba, yakan daskare ya jawo masa ciwo a maransa ya kuma hana maniyin da zai sake tarawa karfi.

7: Ma’auratan da suke da wata matsala na lafiya zasu iya adana maniyin namiji har lokacin da suke bukatar amfani dashi.
Zamani ya zo da ci gaban da masana ke ganin cewa idan aka yiwa namiji aiki zai shafi lafiyar maniyinsa, sai a anada maniyin kamin a masa aiki, yadda bayan aikin ana iya amfani da shi a jikin matarsa domin neman haihuwa.
8: Yanada kyau kuma Maza da Mata mu fahimci cewa, ci gaba na zamani yana yiwa maniyin namiji illa.
Bincike ya gano cewa, su laptop da muke daurawa akan cinyan mu da wayoyin hannun mu suna rage karfi da lafiyan maniyi.
9: Mutane da yawa suna da jahilcin yadda ciki yake shiga mace.
Sau tari ana zargin mace idan tana yawan haihuwan wani jinsi fiye da wani. Misali idan mace ta cika yawan haihuwan mata sai aga tana samun tsangama.
Abunda mutane suka kasa fahimta shine, ita mace aikinta kawai ta ajiye abunda namiji ya tura mata a Mahaifanta, ta raina a cikinta kuma ta haifa.

Mace ba ita ke saka kwan da za a haifi jinsi ba, wannan Yana daga jikin maniyin namiji ne. Amma har sakin mace ake yi wai saboda ta cika haihuwan Maza ko mata, bayan ba laifinta bane laifin mai sakamata kwan ne.
Idan AY ne ya samu shiga cikinta namiji zata haifar. Idan kuma X ne ya shigeta nan kuma mace zata haifa. Haka XY da kuma XX. Amma mace batada ikon haifar jinsin abunda ke cikinta sai abunda mijinta ya saka mata.
10: Abunda wasu ma’auratan basu sani ba shine, a cikin Alkurani Mai Tsarki Allah (SWT) Yayi bayanin yadda maniyi yake shiga cikin mace har ya gina mutum, misalin irin wadannan ayoyin shine (Qur’an 23: 12-14).
Idan Musulmi zai karanta kuma ya fahimci zancen Allah game da yadda Yake halitta mutum bayan mace da miji sunji dadin Jima’i, zai sa mutum ya kara neman kusanci da Allah. Da kuma tabbatar da ikonSa da buwayarSa akan komai.

Wadannan sune wasu abubuwan al’ajabi game da maniyin namiji da akasarin ma’aurata basu sansu ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post