Daf ake da karkare kakar bana ta tamaula, Liverpool wadda ke fatan lashe kofi hudu a bana, saura karawa 11 mafarkinta ya zama gaskiya.
Ranar Asabar Liverpool ta doke Manchester City 3-2 a wasan daf da karshe a FA Cup, hakan ya rage mata kofi uku daga hudun da take fatan lashewa a bana, bayan da ta dauki Caraboa Cup, saura FA da Premier League da kuma Champions League.
Kawo yanzu Manchester United ce a Ingila ta dauki Premier da Caraboa da kuma Champions League a 1999, sai Manchester City da ta lashe kofi hudu a Ingila a 2019 keda tarihin daukar kofuna da yawa a kakar tamaula daya.
Liverpool wadda saura wasa 11 ta cika burinta na lashe kofi hudu a kakar nan, ta lashe Caraboa Cup na bana, bayan da ta yi nasara a kan Chelsea a bugun fenariti
Cikin wasannin da suke gaban Liverpool sun hada da wanda za ta karbi bakuncin Manchester United a gasar Premier League ranar Talata.
Daga nan kuma za ta fuskanci Everton, Newcastle, Tottenham Hotspur, Aston Villa, Southampton da kuma Wolverhampton Wanderers, sannan tana fatan Manchester City ta barar da maki, ita kuwa ta lashe dukkan wasanninta.
Kawo yanzu Liverpool ta yi wasa 12 a jere ba tare da an doke ta ba, sannan ta yi karawa 11 kwallo bai shiga ragarta ba a fafatawa takwas.
Kungiyar da Jurgen Klopp ke jan ragama za ta fuskanci Chelsea a wasan karshe a FA Cup a Wembley ranar 14 ga watan Mayu, sannan ta kara da Villarreal gida da waje a Champions League, wasan daf da karshe.
Sai kuma ta buga wasan karshe ranar 28 ga watan Mayun a birnin Paris, idan ta kai karawar karshen.