Ɗan wasan Denmark Christian Eriksen, mai shekara 30, ya dauki hankalin sabon kocin Manchester United Erik ten Hag. Eriksen a yanzu na zaman kwantiragin wata shida a Brentford wanda ke karewa a karshen kaka. (Star Sunday)
Arsenal ta shirya sabunta kwantiragin ɗan wasan Ingila Tammy Abraham, mai shekara 24, a wannan kaka kuma za ta mika wa Roma tayin £50m a kokarin cimma yarjejeniya. (Star Sunday)
West Ham ta shiga sahun masu gabatar da tayi kan ɗan wasan Torino da Italiya Andrea Belotti, mai shekara 28. (Fichajes - in Spanish)
Real Madrid na kan gaba a fafatawar saye ɗan wasan Jamus Antonio Rudiger, mai shekara 29, wanda ke shirin bankwana da Chelsea a karshen kaka. (Goal)
Rudiger ya ki amincewa da tayin albashin £200,000 a kowanne mako domin ci gaba da zama a Stamford Bridge. (Sunday Telegraph)
Tattaunawa tsakanin wakilan Kylian Mbappe da Paris St-Germain kan sabon kwantiragin matashin ɗan wasan mai shekara 23 na nuna alamomin nasara. (ESPN)
Kocin Barcelona Xavi ya ce yana son ya cigaba da aiki da ɗan wasan tsakiya Frenkie de Jong, wanda ake cewa zai tafi Manchester United saboda sake haduwa da tsohon kocinsa Erik ten Hag. (Manchester Evening News)
Leicester na son daidaitawa da ɗan wasan PSV EindhovenIbrahim Sangare, mai shekara 24. Ɗan asalin Ivory Coast wanda tsadarsa na iya kai wa £30m. (Sun on Sunday)
West Ham za ta yi kokarin sayo ɗan wasan baya Michael Keane daga Everton. (Star Sunday)
Tottenham da Leeds sun tuntuɓi ɗan wasanBristol City Alex Scott, mai shekara 18. (Sunday Mirror)
Arsenal za ta mayar da hankali kan sayo 'yan wasa ɗaya zuwa biyu a wannan kakar, a cewar daya daga cikin jami'anta. (Evening Standard)
Crystal Palace na sanya ido kan ɗan wasan Ingila Malcolm Ebiowei, wanda zai kasance ba shi da kungiya a karshen kaka idan ya yi bankwana da Derby. (Sun on Sunday)
Brentford na fafatawa da West Ham kan sayo ɗan wasan Hull City mai shekara 21, Keane Lewis-Potter. (Football Insider)
Juventus na tuntubar wakilan ɗan wasan ParisSt-Germain mai shekara 34, Angel di Maria. (Gianluca di Marzio - in Spanish)
Aston Villa ta sake nuna azama wajen saye ɗan wasan Marseille Duje Caleta-Car bayan Steven Gerrard ya je ya kalli wasan matashin ɗan shekara 25. (Football Insider)
Napoli na son akalla euro miliyan 80 inda za ta sayar da ɗan wasanta mai shekara 23 Victor Osimhen, yana cikin 'yan wasan na Arsenal ke hari a wannan kakar. (CBS Sports)
Ɗan wasanAtletico Madrid Rodrigo de Paul, mai shekara 27, na son komawa Italiya domin taka leda a Inter Milan. (La Gazzetta dello Sport - in Italian)
Celtic na tattaunawa da Tottenham kan ɗan wasanta na Kamaru, Carter-Vickers, mai shekara 24 a yarjejeniyar dindindin. (SBI Soccer)