A jiya ne sarkin waka wato naziru Ahmed ya fito social media ya nuna bacin ransa matuka ga yadda wasu suke zagin iyayen da suke kawo yayan su almajiranci,
Ni a sau da yawa in na fito social media na yi magana mutane suka cewa ina yi ne don na Bata ma wani rai Wanda ko kadan ni ban taba yin magana don haka ba kuma sannan kawai ina yin magana ne don ba za muga anci mutumcin almajirai mu kyale bah
KUMA yayi banai sosai masu matukar jawo hankalin duk Wanda ya saurara, kadan daga cikin maganganun sarki waka wato naziru Ahmed sune kamar haka
Ya ce da farko de su masu zagin wadannan almajiran wata kila wasu a cikinsu ko Fatiha mai kyau ba za su iya karantawa bah sannan kuma wai su suke fitowa social media don Allah ya basu wata daukaka wadda in suka fadi magana ana ji ta ko ina shi ne suke wanna abun,
Inda ya kara da cewa su masu yin maganganun nan wasunsu da yawa sun ma fi almajirai ai sabado da yawa a cikinsu wasu sunyi kwanan titi amma duk sun manta da hakan basu dubah su irin rayuwar da suka shigah sai almajirai masu karanta Alqur'ani za su xo suna zagi
Ya kuma dada da cewa duk Wanda kagah yana bara to fah ba wai yinsa ba ne shima a dole ya ke yin hakan don kuwa inda ya na da yadda zayyi sai dai yayi ta tara kudin amma ba zai temaki mutane ba kuma ya ce, su wadanda a ke amfani da su din suke zuwa suke yada maganganun da yawan su iyayensu suma son zuciya ne ya saka suke barsu don ba iyayen kirkin da za su bar yayansu a gidan wani yau su kwana a wancan hotel din ko wani waje na daban inda ba a san gunda suke ba sannan kum wai da sunan sana'a.
Kuma ya dada da cewa ai ba haka ya kamata a yi musu bah kamata yayi in mutum yasan xai yi haka sai ya debesu ya gina musu makaranta ko dai ya na ba su abincin kaman yadda ya kawo musalin yadda wata mata tayi amma kuma ita ma bai ambaci sunanta bah, raina ya baci matuka ganin wannan labari da nayi yana ta yawo a social media don nima na yi almajiranci xa a bani sile biyu ko uku kullun amma kuma ni ana bani abinci a gidanmu, har mah ya kawo musali gunda ya kai matarsa ya nuna mata inda yayi almajiranci ya ce ranar da aka kawoshi a taburma ya kwana Wanda kuma shi bai ma santa bah, don ko barci bai iya ba ranan, kuma da yawa a cikin masu karanta Alqur'ani din na wasu da yawa sunfi gidansu ma kudi kaman yadda yadda ya aiyana ya ce dukda shima gidansu ba matsiyata ba ne iya kudi tun da dama Allah ya hore musu.
Inda ya kara da cewa duk masu zagin babu mai iya bada naira millions dari don a Gina ma su almajirai Makaranta,dagah karshe ya jawo hankalin manyan celebrities da kuma bloggers da a daina amfani da su wajen yada karya ko kuma irin wadannan abubuwan da basu da ce bah.
A nan ne .muka kawo muku karshen labarin inda ni yakubu abdulhamid na yi rubutun zube Wanda kuma wannan website www.nairaside.com.ng ya dauki nauyin kawo muku. Ku ci gaba da biyomu don min samun labarai kamar haka
Tags:
KANNYWOOD