Abun da ya sa mutum ya ke kyakyata dariya

Tattaunawata da Sophie Scott ta kusan zuwa ƙarshe loakcin da ta matso gaba daga kan kujerarta tana nuna min hoton wani mutum tsira-tsirara yana tsindimawa cikin kogin wanka na alfarma.

Bayan ya shafe kamar minti ɗaya yana mommotsa hannayensa, sai ya tsunduma - amma sai ya faɗa kan wani ƙwallon ƙanƙara. Ruwan bai motsa ba amma abokansa ba su yi wata-wata ba wajen ɓarkewa da dariya.

"Suna ganin babu jini sai suka ɓarke da dariya," a cewar Sophie. "Suna ta ɓaɓɓaka dariya da shewa; sun kasa dainawa."

Me ya sa muke fuskantar irin wannan yanayin na dariya - ko a lokacin da wasu ke fama da raɗaɗi? Kuma me ya sa muka kasa dainawa?

Yayin da ƙwararriya kan ƙwaƙalwar ɗn Adam Sophie ke ƙoƙarin amsa waɗannan tambayoyi a shekaru da suka gabata - ta yi jawabi a Vancouver a makon da ya gabata kan dalilin da ya sa dariya ke da muhimmanci da kuma yadda aka kasa fahimtar ta.

Abokan aikin Sophie ba su goyi bayan aikinta ba a kodayaushe. Tana so ta yi magana kan wani rubutu da ta gani a cikin takardunta. "Wannan tarin takardun shara ce kawai (saboda yanayin takardun) kuma za a zubar da su ne idan ba a kwashe su ba," kamar yadda aka rubuta a takardun. "Wannan kimiyya ce?"

Yanzu kuma Sophie na sanye da wata t-shat ɗauke da rubutun wata tambaya da ke cewa ko kun shirya zuwa wani wasan barkwanci da take son shiryawa da dare.

"Za ku iya samun ganin jinsina, da shekaruna, da arzikina, da asalin inda na fito, da yanayin mu'amalata, da lafiyata, da kuma ma abubuwan da suka shafi hira," a cewarta.



Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus


Ɗaya daga cikin ayyukanta shi ne ta nazarci yadda mai sana'ar kwaikwayon mutane Duncan Wisbey ya saba da kwaikwayon jawaban mutane. Ta gano cewa ƙwaƙwalwa na haska daidai yadda jiki ko motsi da jikinsa yayin da yake ƙoƙarin aikata duk abin da wanda yake kwaikwaya yake yi. Aikin gano masu kwaikwayo ya taimaka mata wajen gano yadda mutane ke da yaruka da karin harshe daban-daban.

Sai dai wani bincike da aka yi ne a Namibia ya sa Sophie ta gano cewa dariya ɗaya ce daga cikin mafiya muhimmanci kan yadda ƙasusuwanmu ke motsawa. Bincike ya nuna za mu iya gane hanyoyin ji da ɗan Adam ke amfani da su - tsoro, fushi, mamaki, takaici, ɓacin rai - ta hanyar yanayin fuskar mutum. Sophie na son ta gano ko za mu gano wasu bayanai daga muryar mutum.

Saboda haka sai ta tambayi 'yan Namibia da kuma Turawa mazauna ƙasar da su saurari maganganun juna kuma su bai wa abin da suka ji maki - ciki har da hanyoyin ji da aka amince da su.

Dariya ce abin da ɓangarorin biyu suka fi ganewa da sauri. "Kusan nan take ake iya bambance dariyar da sauran abubuwa masu amfani," a cewarta.

Yayin da take ƙara gano abubuwa tana kuma ƙara yin mamakin abin. Don da nan ta gano cewa akasarind dariyard a ake yi ba tad a aaƙa da barkwanci. "Mutane na yawan tunanin cewa suna yi wa barkwancind a sauran mutane suka yi dariya ne, amma mutumnin da ya fi yi wa mutane dariya shi ne ya fi yawan yin magana," a cewarta.

A madadin haka, tana kallon dariya a matsayin "yanayi na al'umma" da ke taimaka mana yin mu'amala da juna, game da ko wani abu na dariya ne ko ba akasin haka. "Idan kuka yi dariya tare da mutane kuna nuna musu cewa kuna son su, kun yarda da su, ko kuma kuna cikin rukuni ɗaya tare da su," in ji ta. "Dariya ce ƙololuwar sirrin alaƙa tsakanin al'umma."

Dariya mai yaɗuwa

Wannan na iya bayyana yadda ma'aurata ke yi wa juna dariya - yayin da su kuma masu kallonsu ba sa jin dariyar. "Za ku ji wani na cewa 'yana da barkwanci kuma gaskiya dalilin da ya sa yake burgeni kenan'. ABin da kake nuifi shi ne 'yana burge ni, na san shi kuma ina nuna masa cewa yana burge nin ta hanyar yin dariya duk lokacin da muke tareda shi'".

Tabbas dariya ka iya zama abu na farko da ke kyautata alaƙa, in ji ta tana mai ambato wani bincike. Ta ce ma'auratan da ke ɓaɓɓaka dariya da juna na da damar magance wata damuwa bayan sun shiga matsanancin halin aiki.


Yanzu Sophie na da sha'awar gano bambanci tsakanin 'yar dariya da muke yi yayin hira da kuma wadda ke suɓucewa mu ƙyaƙyata, har ma takan ɓata shirin talabijin da rediyo.

Misali, ta ce 'yar dariyar da ake yi da gangan an fi yinta ne daga hanci, yayin da ita kuma wadda ke suɓucewa mu ƙyaƙyata ba daga hanci take fitowa ba.

Wani hoton ƙwaƙalwa da ta nazarta ya nuna yadda ƙwaƙalwa ke mayar da martani wajen yin kowace irin dariya. Dukkan hotunan sun nazarci yadda ake kwaikwayon aikin wani mutum. Yankunan ƙwaƙalwa kan motsa idan na gan ka kana buga ƙwallo ta yadda zan ji ko ni ne zan buga ta da kaina - kuma irin yanayin ne ke sa dariya ta suɓuce mu yi ta ƙyaƙayatawa.

Za ku iya tunanin cewa bambance dariya ta gaske da ta gangan abu ne mai sauƙi. Sai dai Sophie na ganin ƙwarewa ce da ke samuwa a ɗabi'unmu da ba ta samuwa har sai mun kai shekara 30 da wani abu da haihuwa. Wannan dalilin ne ya sa ta kafa wani wurin bincike a Landan, inda za ta dinga neman baƙi su dinga nazartar ingancin dariyar mutane da kuma kukansu.

Ta ƙaa da cewa kuka ya fi zama wata hanya da yara ke amfani da ita wajen aika saƙo, yayin da su kuma manya suka fi amfani da dariya.

Duk da cewa ba mu fiya son yadda mutane ke yin dariyar boge ba, Sophie na ganin hakan ya fi bayyana abubuwa game da mu fiye da a kansu da kuma yadda muke ji game da salon rayuwarsu, ba wai wani abin ƙi ne game da rayuwar tasu ba.


Sai dai kuma, ta ce masu wasan barkwanci sun fi samun sauƙi wajen yin wasanni a bainar ɗaruruwan jama'a saboda yanayin da ake shiga na nufin dariya ta fi kama nan da nan idan akwai mutane da yawa a wurin.

Zuwa yanzu, ta yi ƙoƙarin samar da na'urar bin diddigi ga masu kallon wasannin barƙwanci don bin sawun ɓarkewar dariya - masu kallon ba sa son yin hakan. Amma tana fatan ci gaba da aiki da manyan 'yan wasan barkwanci kamar Rob Delaney, wanda ka iya yin hakan.

Sashen BBC Future ne ya shirya shi.

Post a Comment

Previous Post Next Post