ni wllah bantaba Shan kwayaba ko kadan Kuma bana fata nasha Kuma Ni idona ahaka yake


Daya daga cikin jarumai mata acikin masana’antar Kannywood Aisha Najamu izzar so ta bayyana cewar bata ta’ammali da kayan maye kama daga kwaya kokuma wani abu wanda idan mutum yasha hankalinsa zai gushe domin ta aikata wani abu da akeso acikin film.

“Aisha Najamu izzar so ta bayyana cewar inda ace tanashan kwaya kokuma wani abun maye to bazata dingayin ayyukanta dakyau kamar yadda ake bukata daga wajan darakta, ta kara bayyana cewar indai har mutum yanshan kwaya ai bazai iya rike abind akeso ya fada ba”.

“Aisha Najamu takara bayyana cewar yanayin yadda takeyin (acting) acikin shirin wasan Hausa haka halittarta take, ahakan ma takara wasu abubuwa domin tabawa darakta abinda yakeson gani a tattare da ita”.

Post a Comment

Previous Post Next Post