Najeriya yadda rashin lantarki ke kassara tattalin arzikin kasar

Yan Najeriya sun sake tsintar kansu cikin yanayi na rashin wutar lantarki a wasu sassan kasar da dama, abin da ya jefa su cikin duhu da korafe-korafe kan yada rashin wutar baki daya ke shafarsu da sana'arsu.

A wannan lokacin mahukunta na cewa matsalar rashin wutar lantakin na da nasaba da katsewar babban layin lantarki na kasa a Najeriya. Sai dai wannan shi ne karo na hudu da ake fuskantar wannan matsala a watanni biyu a jere.

A baya mahukuntan kasar sun danganta al'amarin kan masu fasa bututan mai da ke jihar Bayelsa a yankin kudu maso kudancin kasar.

Babban layin wutar lantarkin ya dogara kacokan a kan iskar da ake samar masa daga bututun man na Bayelsa kuma a duk lokacin da aka samu matsala to hakan na kawo cikas wajen samar da wutar lantarki ga kasar baki daya.

Duk da cewa babu cikaken bayani a kan ko mene ne ya janyo katsewar wutar lantakin a wannan karon, ma'aikatar wutar lantaki ta kasar ta ce matsalar da aka samu a babban layin wutar lantarki na kasar a ranar 18 ga watan nan na Afrilu ta sa an kara samun raguwar wutar da ake da ita da megawat 903 daga cikin wanda ake da shi.

Sanarwar ta ce a ranar 17 ga watan Afrilu kasar ta rika samar da megawat dubu 3,829 amma a washegarin ranar ta ragu zuwa 2,926 saboda matsalar da ta samu.

Hakan ya janyo karancin wutar a fadin kasar kuma 'yan Najeriya da dama musaman masu harkokin kasuwanci sun koka a kan yadda yawan daukewar wutar lantarki ke kassara harkokin kasuwancinsu.

Wata mata mai sana'ar gyaran gashi a birnin Kano ta shaida wa BBC matsalar ta fi kamari a ungwar da suke zama.

"A inda muke ba ma samun wuta kwata-kwata, idan an samu ma sai cikin dare kuma a lokacin duk wani mai aiki ya kulle wurin aikin shi."

Shi ma wani mai sana'ar dinki ya ce a bana zai wuya su cika alkawuran dinkin saboda yawan daukewar wutar lantakin.

"Aikin da ya kamata mu yi a cikin kashi 100, yanzu bai wuce mu iya yin kashi talatin ba ko kashi 20," in ji shi.

A baya sai da Shugaba Muhammadu Buhari ya bai wa 'yan Najeriya hakuri kan daukewar wutar lantarki inda ya ce gwamnatinsa ta dauki matakan gyara sai dai ga dukkan alamu matakan ba sa yin tasiri sosai. A nan NE muka kawo muku karshen labarin Wanda wanna website mai suna www.nairaside.com.ng ya dauki nauyin kawo muku.

Post a Comment

Previous Post Next Post