ANAN KUMA ZA KUJI CEWA ANA TA ZANGA ZANGA AKAN WANI BABBAN DAN SIYASA DA YA KYAMACI MUSULINCI YA KONA ALQUR'ANI A SWEDEN.
Mummunan rikici ya barke a kasar Sweden a makon nan a birnin LinkΓΆping da ke gaΙar tekun gabashin Ζasar, inda aka yi arangama tsakanin Ζ΄an sanda da masu zanga-zanga da suka fito domin nuna fushinsu kan Ζona Al Kur'ani mai tsarki da wani dan siyasa mai tsaurin ra'ayi ya yi a wani gangaminsa.Rahotanni sun ce Ζ΄an sanda uku suka jikkata.
Mutane sun sake fitowa zanga-zangar, a cewar hukumomin birnin Orebro da ke tsakiyar kasar, bayan wani gangami na nuna Ζyamar baΖi da kuma addinin Islama ΖarΖashin jagorancin mai tsattsauran ra'ayi Rasmus Paludan Ιan siyasa mai asali biyu Denmark da Sweden. A yayin zanga-zangar ‘yan sanda tara suka jikkata.
An kama mutum biyu a lokacin zanga-zangar. Ζ³an sanda sun nuna cewa aikinsu shi ne su tabbatar da Ζ΄ancin mutane na bayyana ra'ayinsu, don haka ba haΖΖinsu ba ne su zaΙi wanda yake da gaskiya.
Baludan ya daΙe yana haifar da ruΙani da ce-ce-ku-ce. A watan Nuwamban 2020, hukumomin Faransa sun kama shi tare da korarsa daga Ζasar. Wanda www.nairaside.com.ng ta kawo muku.