katin gayyatar yan takara da Aisha Buhari TA yi ya jawo cece ku ce a najeriya

Sunan Aisha Buhari, matar Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, na ta waɗari a bakunan 'yan ƙasar musamman a shafukan zumunta tun bayan da ta gayyaci 'yan takarar shugaban ƙasa na dukkan jam'iyyu zuwa buɗe baki.

Babban abin da ya fi jan hankalin 'yan ƙasar shi ne umarnin da ta bayar a katin gayyatar cewa "ba a yarda ku zo da wayoyinku ba".

'Yan takara irinsu Atiku Abubakar da Bola Ahmed Tinubu da Nyesum Wike da Farfesa Yemi Osinbajo da Chris Ngige da Bala Mohammed da David Umahi da Rochas Okorocha aka gayyata da kuma ba su umarta da kada su je da wayoyin nasu.

Kafofin yaɗa labarai a Najeriya sun yi imanin cewa matar shugaban ta koma ƙasar ce daga Daular Larabawa a farkon wannan makon gabanin tura gayyatar.

"Da gaske Aisha Buhari na gayyatar manyan mutane kar su je buɗe baki tare da wayoyinsu, wannan ai tashin hankali ne," in ji wani mai suna Dumbshroom @Dumbshroom_.

Su wa Aisha Buhari ke gayyata?

ASALIN HOTON,FACEBOOK/AISHA BUHARI

Bayanan hoto,

Aisha Buhari ta yi buɗe baki tare da matan 'yan majalisar wakilai da kuma na shugabannin tsaron ƙasar a ranakun Laraba da Alhamis

Wani katin gayyata da kafofin yaɗa labarai suka wallafa ya nuna yadda mai ɗakin shugaban ta gayyaci dukkan 'yan takarar shugaban ƙasa daga jam'iyyun siyasar ƙasar.

A cewar gayyatar, liyafar buɗe bakin za ta gudana ne ranar Asabar 23 ga watan Afrilu a Ɗakin Taro na Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja da ƙarfe 6:30 agogon ƙasar.

"Muna roƙunku ku taho da wannan katin amma ba a yarda a shiga da waya ba," kamar yadda aka rubuta a katin gayyatar.

Abin da ya fi jan hankalin 'yan Najeriya

Masu amfani da intanet a Najeriya sun nemi ƙarin bayani kan Aisha Buhari a shafin matambayi-ba-ya-ɓata na Google sau fiye da 10,000 a ranar Juma'a.

Mazauna jihohin Kebbi da Katsina da Yobe da Borno ne kan gaba a neman ƙarin bayanin, yayin da sunan nata yake mataki na biyar cikin waɗanda suka fi tashe a Najeriya.

Akasarin waɗanda suke ce-ce-ku-ce kan batun sun fi mayar da hankali ne kan batun kada a je da waya.

Sai dai mai taimaka wa Aisha Buhari kan kafofin yaɗa labarai, Aliyu Abdullahi, ya faɗa wa wata kafar yaɗa labarai cewa hana shiga fadar shugaban ƙasa da waya ba sabon abu ba ne.

"BBC Hausa kun manta ba ku ce ta gargaɗe su kada su je da waya ba," in ji Baballiya a shafinsa na Twitter.

Wani ma'abocin shafin BBC Hausa a Twitter bai fahimci matsayin Aisha Buhari ba, yana mai cewa "alƙawarin mijinta ne ba zai yi (muƙamin) first lady ba".

Shi kuwa Ahmadu Abacha a shafin BBC Hausa na Facebook, ya ga dacewar gayyatar da Aisha ta yi.

Post a Comment

Previous Post Next Post