kasuwar yan kwallo Arsenal na San tattaunawa da gabrel Jesus dan Manchester city kuma dan ainshin kasar ta Brazil👇👇👇

Arsenal na son dauko É—an wasan Manchester City Gabriel Jesus, mai shekara 25, zuwa Emirates, tuni kuma wakilan Æ™ungiyar suka soma tattaunawa da É—an wasan dan asalin Brazil.(Athletic, subscription required)

Mo Salah na son ci gaba da zama a Liverpoolsai dai akwai rashin tabbas kan makomarsa a gaba ganin har yanzu ba a cimma yarjejeniya ba kan kwantiraginsa, kuma É—an wasan mai shekara 29 asalin kasar Masar na cewa Kudi ba ita kadai ba ce abin dubawa. (Four Four Two)

Paris St-Germain ta gabatar da tayin euro miliyan 50 kan É—an wasan Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 23 a shekara, hakan zai sa ya kasance É—an wasa mafi tsada a Æ™ungiyar. Akwai É—an matsalar kan batun komawarsa Real Madrid kan abin da ya shafi 'yanci. (Goal)

Mahaifiyar Mbappe da wakilinsa Fayza Lamari na tattaunawa a Qatar da mai kungiyar PSG(Le Parisien - in French, subscription required)

Kocin Tottenham Antonio Conte ya matsu ya koma horar da PSG a kaka ta gaba kuma yana da kwarin-gwiwar zai iya maye gurbin Mauricio Pochettino a Parc des Princes. (Le Parisien - in French, subscription required)

Newcastle na shirin daukan mai tsaron ragar PSG Keylor Navas, wanda zai yi bankwana da kungiyar da ke jan ragama a Ligue 1a wannan kakar, sai dai É—an wasan mai shekara 35 asalin Costa Rica ya lasawa Juventus da Sevilla zuma a baki. (Fichajes - in Spanish)

Declan Rice ya sake yin watsi da tayin West Ham karo na uku kan albashin £200k a kowanne mako. Duk da cewa Æ™ungiyar ta dage kan cewa É—an wasan ba na sayarwa ba ne za ta iya karban fam miliyan 150 kan É—an wasan mai shekara 23 daga hannun masu farautarsa Manchester United da Chelsea(The Guardian)


Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Tottenham ta tattauna da Inter Milan kan saye É—an wasan Netherlands Denzel Dumfries, mai shekara 26. (Tuttosport, via Sport Witness)

Celtic ta shiga wani mataki a tattaunawarta da Tottenhamkan saye É—an wasanta na baya Cameron Carter-Vickers, mai shekara 24. (SBI Soccer)

An sanar da wani É—an wasan TottenhamJoe Rodon mai shekara 24, cewa yana iya barin kungiyar. (Football Insider)

Newcastle na bibiyar É—an wasan Monaco Benoit Badiashile, da kuma na Bayer LeverkusenMoussa Diaby, mai shekara 22. (Foot Mercato)

ÆŠan wasan Chelsea Antonio Rudiger ya nuna cewa babu batun tafiya Manchester United(Ben Jacobs, CBS)

Wayne Rooney ya yi watsi da tayin Erik ten Hag da ke son su yi aiki tare a Manchester United, ya dage kan cewa zai iya barin Derby County ne kaÉ—ai domin aikin horaswa. (Athletic, subscription required)

Fulham na son dauko dan wasan Lazio Sergej Milinkovic-Savic mai shekara 27.. (90 Min)

Tsohon É—an wasan Manchester UnitedWest Ham da Manchester City Carlos Tevez na iya bada mamaki ya dawo fagen tamaula bayan shekara guda, rabon É—an wasan mai shekara 38 ya taka leda tun wasan da ya bugawa Boca Juniors. Dan wasan mutumin Argentine ya ziyarci AC MilanJuventus da Tottenham da kuma kungiyarsa West Ham. (Goal)

Leicester da Aston Villa na zawarcin tsohon É—an wasan Manchester City da Fulham loanee Seko Fofana, mai shekara 26. ÆŠan kasar na Ivory Coast yanzu haka na zaman aro a Lens(But! Football Club)

Barcelona ta kawar da wata alamar za ta tuntubi É—an wasan Arsenal Gabriel Magalhaes, mai shekara 24, saboda dalilai na kudi. (Mundo Deportivo)

Post a Comment

Previous Post Next Post