Wani karin damar ga Benzema shine ya dauki hanyar lashe kyautar Ballon d’Or na bana, saidai Mohamed Salah na Liverpool ka’iya kawo masa hamayya idan Liverpool din ta dangana ga buga wasan karshe.
Ga wasu daga cikin mafi kyawun martani daga magoya baya akan Karim Benzema wanda yakai Madrid ga nasara:
Rio Ferdinand ya yi imanin Sir Alex Ferguson ya yi nadamar rashin kawo Karim Benzema zuwa Manchester United
Kafin karawar da aka yi a babban birnin Spain, tsohon dan wasan baya na Manchester United, Rio Ferdinand, ya bayyana cewa Karim Benzema ne dan wasan gaba a duniya a halin yanzu. Ya kuma yi ikirarin cewa Sir Alex Ferguson ya yi nadamar rashin sayen dan wasan a shekarar 2009.
Da yake magana a matsayin masani kan BT Sport, kamar yadda The Mail ta ruwaito, Ferdinand ya ce:
“Lokacin da na buga wasa da shi na gane nan da nan shi babban dan wasa ne.
“Benzema yana daya daga cikin ‘yan wasan da Sir Alex baiji dadi ba da bai samu ba.”
Tun daga shekara ta 2009 Benzema ya zura kwallaye 317 a wasanni 597 da ya yi wa Real Madrid. Ya kuma kasance babban memba a kungiyar da ta lashe gasar zakarun Turai hudu a cikin shekaru biyar.
Ferdinand ya kuma yi imanin cewa dan wasan yana taimakawa ci gaban dan wasan gefe Vinicius Junior, mai shekara 21, wanda ya yi fice a kungiyar. Ya kara da cewa:
“Ba shi da wani misali da ya fi Benzema. Benzema ya dauke shi a karkashin reshen sa. Suna da alaka a yanzu mai kyau. manyan kocha koccen nafadin cewa benzema zai I lashe kyautar balandi'o