KARIM BENZEMA YACE INAJIN DADIN KASANCEWA TA A REAL MADRID A KOWANNE RANA

Benzema ya ci gaba da zama babban jagora mai daukar nauyin samun nasarar Real Madrid. Nairaside.com.ng 

Karim Benzema ya taka rawar gani a karawar da suka yi da Chelsea, inda ya zura kwallo mai ban mamaki, duk da haka an bayyana cewa kocinsa dan kasar Italiya bai yi mamakin irin yadda tsohon dan wasan na Lyon ya yi a kakar wasanni uku da suka gabata ba

Ancelotti ya kara da cewa” aikinsa ya dade yanayin kyau sosai, yana ci gaba da ingantawa.”

“Ya inganta a filin wasa da bayan wasa, a cikin jagorancinsa, shekarun Karim ba su da wani bambanci ga abokan wasansa da yake da su, a nan gaba zai kasance daya daga cikin manyan ‘yan wasa a wannan kungiya.

“Yana da abubuwa na musamman da yawa, ya zama cikakken jagora, kuma dan wasa mai kyau da ya kasance koyaushe.”

Karim Benzema ya zura kwallaye uku sau biyu ajere bayan ya kori Paris Saint-Germain, a wannan makon ya zurawa Kungiyar Chelsea uku itama, hakan yasa Dan wasan ya zura kwallaye 11 a wasanni 8 a gasar Zakarun Turai na bana.

Tura zuwa wani..

Post a Comment

Previous Post Next Post