INDAI KA KARANATA WANNAN KUMA KA FAHIMTA TO WAHALAR KA TA KARE A FOREX, DA CRYPTO MARKET

KASUWAR FOREX (BULLISH🐃 & BEARISH🐼)*

A Forex yanayin da ake samun kasuwa a yanayi 3 ne, Kuma ko wanne yana yi da yadda ake gabatar da salon kasuwancin shi.

   *UPTRADING MARKET⬆📈*

Wannan yanayi ne da zaka samu kasuwa Tana Sama, kenan tana Tafiya a Turba daya, Wato Farashi Yana Hawa sama (Bullish Market)

*DOWNTRADING MARKET⬇📉*

Wannan yanayi yana Nufin Farashi kasuwa Kasa yake, wato (Bearish Market)

*RANGING MARKET (Consolidation)*


Wannan yanayi ne mai Hatsari a kasuwar Forex, sabida ba wani Trader da zaice ma wannan kasuwa ga inda ta nufa, ita irin wannan kasuwa kawai tana Hargitsi ne tsakanin *Bullish📈* da kuma *Bearish📉* Anan zaka tsaya ne ka jira su gama Fadan su, Lokacin da kaga daya yapi karfin daya, to sai ka shiga sai ka goyawa mao Karfin baya.


*Misali* Bullish🐃 ne yafi karfin Bearish, to sai ka koyawa Bullish🐃 baya a cigaba.
Idan kuma Bearish🐼 ne yafi karfi, to nan ma sai ka goyawa Bearish🐼 baya a cigaba, Kai dai kawai ko yaushe kana Goyan bayan wanda yafi karfi.


  *SUWAYE BULLISH🐃 DA BEARISH🐼*


  Asalin sunan Bullish⬆ an samo shi ne daga SA🐃 namiji Saniya.

Dalilin dayasa aka saka musa Bullish📈⬆ kuwa shine kamar yadda *SA🐃* idan ya dauki abu da kahon shi yake wulli dashi sama suma wadannan bullish📈 din haka suke daga Farashin kasuwa tayii sama....

    Sai kuma Bearish🐼 shima sunan ya samo asali ne daga wata dabba da take turmumusa Abokin fadan ta a kasa...

Ta wannan ne aka samu bearish📉 dan dabi'ar su ta sauke Farashin kasuwa kasa a duk lokacin da suka bayyana...

    Toh kasuwar Forex Fadane tsakanin Bearish🐃 da Bullish🐼...Kai kuma dan kasuwa ba rabawa ake so kayi ba.

zaka duba ne kaga wanda yafi karfi sai ka goya masa baya...
    Idan Farashi hawa yake ka *(BUY)* idan sauka yake kayi *(SELL)*.

Kamar yadda na fada muku a farko Class din nan, Ita kasuwar Forex. Ana jifan tsuntsu biyu ne da Dutse daya, idan Faduwa take kai Lapiya lau, Haka idan hawa sama take Lapiya lau a wajen ka, Amma idan ka riga ka shiga kasuwa to dole fa, anan matsalar take,,,


*MISALI* Da farko ka shiga kasuwa kana tinanin Faduwa kasuwa take, sai kuma tazo ta tashi sama, Tofa kai Sai dai muce, Allah ya maida alkhairi.


Haka ma idan kana Tinanin cewa kasuwa Sama⬆ take, sai ka shiga daga baya sai tazo ta fara faduwa⬇ to, nan ma zamuce ma Allah ya mai da Alkhairi😂. Ku ci gaba da biyomu ta wanna website mai suna www.nairaside.com.ng domin ci gaban darasin namu sannan kuma ku tura ma sauran yan uwa hausawa domin amfanin kowanmu

Post a Comment

Previous Post Next Post