ANA BINCIKEN RONALDO KAN FASA WAYAN DAN KALLO

Yan Sandan Merseyside na bincikar dan kwallon Manchester United, Cristiano Ronaldo, wanda ake zargi ya fasa wayar dan kallo.

Wani bidiyo da yake yawo a kafar sada zumunta dauke da sako, ya nuna lokacin da ya kwada wayar da kasa, bayan da United ta yi rashin nasara da ci 1-0 a gidan Everton.

Daga baya Ronaldo mai shekara 37 ya nemi afuwa a kafar sada zumunta.

'Yan Sandan Merseside sun ce suna binciken ''rahoto kan zargin cin zarafi'' da aka yi a filin Goodison Park ranar Asabar.

Jami'in da ke magana da yawun jami'an tsaro ya ce suna tattaunawa da Manchester United da kuma Everton kan lamarin.

''A lokacin da 'yan wasan ke barin fili da misalin karfe 2.30, an yi rahoton cewar an ci zarafin wani yaro daga wajen wani dan wasa baki a lokacin da za su bar filin.'

''Ana kan bincike kuma jami'ai na aiki tare da mahukuntan Everton da neman faifan bidiyon da aka nadi lamarin da ganawa da shaidu, domin tabbatar da hujjar abin da ya faru.''

''Ana neman duk wanda yake da shidar kan abin da ya faru da ya tuntubi 'Yan Sandan Merseyside a kafar sada zumunta a Twitter MerPolCC ko kuma ta Facebook Merseyside Police, sai a tuntuba ta binciken da aka yi wa lamba 228 na ranar 9 ga watan Afirilun 2022.''

Manchester United ta ce ta san da ''zargin da ake yi'' sannan za ta bayar da hadin kai kan binciken da 'yan Sanda ke yi.

Bayan da aka ci United hakan ya kawo mata cikas kan neman gurbin shiga Champions League a badi, bayan da Everton ke fatan kaucewa daga faduwa daga Premier League ta bana.

Sai dai Ronaldo dan kwallon tawagar Portugal ya ce ''Yana da wahala ka boye fushinka a irin halin da muke ciki.

''Koda yake dole muke martabawa da hakuri, da kuma yin halayya ta gari da yara za su kwaikwaiya masu sha'awar tamaula.

''Ina son na nemi afuwa kan fusata da na yi, kuma idan da hali, zan so na gayyaci magoyin bayan domin ya kalli wasa a Old Trafforrd.

Post a Comment

Previous Post Next Post