Tauraron dan kwallon Barcelona, Dani Alves, ya ce Manchester City za ta lashe gasar zakarun Turai a bana. Nairaside.com.ng ta rahoto.
Sky Blues, wacce ta sha kashi a wasan karshe a hannun Chelsea a bara, tana matakin daf da na kusa da karshe, inda ta yi nasara a kan Atletico Madrid da ci 1-0.
Yayin da aka soke dokar cin kwallaye a waje, Rojiblancos, zakaran gasar Sipaniya, za su kasance da kwarin gwiwa cewa za su juya wasan.
Sai dai Alves yana ganin ba wai kawai City zata samu damar zuwa zagaye na gaba ba, a’a, harma za ta ci gaba har zuwa daukar kofinta na farko a Turai.
Da yake magana da Mundo Deportivo, ya ce:
“Ina ganin haka, kuma su ne ‘yan takara na gun lashe gasar Zakarun Turai.
“Su ne ƙungiyar da ke da mafi kyawun yan wasa da mafi kyawun ra’ayi na yadda ake wasa da lashe gasa da yadda ake yin abubuwa. Ni mai son Pep Guardiola ne, duk abin da ya yi, zan yi godiya.”
Duk da kasancewar ta mamaye fagen cikin gida a karkashin Guardiola, City ba ta iya samun kwarin gwiwa a matakin Turai ba.
Sun tsallake zuwa gasar cin kofin zakarun Turai zagaye na 8 sau daya kacal a karkashin dan wasan na Sipaniya, yayin da suka sha kashi a hannun kungiyoyi kamar AS Monaco, Lyon da Tottenham Hotspur.
Idan aka yi la’akari da yanayin da suke ciki a yanzu, Sky Blues na cikin wadanda aka fi ganin zasu lashe gasar ta bana, amma suna fuskantar babbar hanya kafin zuwa gaba.
Idan har suka doke Atletico, akwai yuwuwar zasu kara da Real Madrid a wasan kusa da na karshe kuma za su iya karawa da Liverpool ko Bayern Munich a wasan karshe a Paris idan suka isa can.
Alves, wanda ke gab da komawa Etihad a shekarar 2017 bayan ya bar Barcelona, ya kasance wani muhimmin bangare na kungiyar Guardiola ta Barcelona wadda ta lashe kofuna tsakanin 2008 da 2012, ciki har da gasar zakarun Turai a 2009 da 2011.