ABUNDA YASA MASU GATIN FILIN CHELSEA SUKA HANA BENZEMA SHIGA FILIN

Karim Benzema ya girgiza zukatan dukkan magoya bayan Chelsea da ‘yan wasan gaba daya, kuma abubuwa sun iya bambanta sosai a yammacin London a makon da ya gabata bayan anbar dan wasan ya shiga filin Stamford Bridge. Nairaside.com.ng 

An dakatar da dan wasan na Faransa a wajen kofar shiga filin saboda ba ya dauke da takardar shaidar da ta dace ya shiga filin wadda yan wasa ke nunawa su wuce a lokacin da ya sauka daga motar bas din kungiyar gabanin wasan daf da na kusa da karshe na gasar zakarun Turai.


Los Blancos ce ta jagoranci wasan daf da na kusa da na karshe da ci 3-1 inda Benzema ya zura kwallaye uku, wanda shi ne adadi na biyu a gasar zakarun Turai a jere, kafin Benzema ya shiga wannan filin saida kocin kungiyar Carlo Ancelotti suka yi ta zage-zage, ya samu damar shiga Stamford Bridge.

Tuni dai Benzema ya yada bidiyon lamarin a shafinsa na Instagram kuma kociyan nasa ya yi magana akai.

“Kafin wasan, Benzema ya kasa samun fas dinsa don shiga filin wasa, sai na ce masa ‘ka yi sauri ka nemo fas dinka inba haka ba, Ba za ka iya buga wasa ba!’ sannan kuma, aka yi sa’a, Karim ya sami fas dinsa a cikin jaka,” Ancelotti ya shaida wa Amazon Prime.

Kawo yanzu “Karim Benzema yana samun jindadi a kowace rana; kamar yadda yake fafatawa a kakar wasansa mafi kyau a rayuwarsa. yana jin dadi sosai a cikin wannan tawagar ta Real Madrid.

“Yanuna hazaka da yawa, ya san shi dan wasa ne mai matukar muhimmanci a gare mu kuma shi ne abin koyi ga kowa.” Inji Ancelotti

Tun daga farko kakar wasa, Benzema har zuwa gab da karshe yana tafiya da karfinsa

Tun bayan shan kashi da ci 1-0 a Paris, Benzema bai buga wa Real Madrid wasa daya kacal bane kawai shine- Clasico da suka sha kashi a hannun Barcelona da ci 4-0.

Real Madrif ta lashe sauran wasanni takwas a wancan lokacin, inda Benzema ya fara a dukkanin su ya kuma zura kwallaye 13.

Post a Comment

Previous Post Next Post