Wani fitaccen dan fim a Tunisia Mohamed Al-Siyari ya haifar da ce-ce-ku-ce musamman a Gabas Ta Tsakiya bayan ya yi kiran a dawo da yin azumi lokain hunturu duk shekara.
Ya yi wannan tsokacin ne a wata tashar rediyo ta Shams FM a Tunisia a ranar Juma'a.
A tattaunawar, ya ce ya kamata "Ramadan a mayar da shi watan Disamba duk shekara, saboda azumi lokacin bazara akwai wahala," yana kuma mai cewa "mayar da yin azumi lokacin hunturu zai Ζarfafa wa mutane yin azumi. "
Ya jaddada ra'ayinsa da cewa "addini mai sauΖi ne ba wahala ba" tare da yin tambayar cewa: "Me ya sa wai muke azumi cikin tsananin zafi?"
Ramadan wata ne na tara a kalandar Islama, kuma wata ne mai alfarma da Musulmai ke shafe tsawon watan suna Ibadar azumi, Ιaya daga cikin shika-shikan Musulunci.
Amma al-Siyari ya ce ya kamata malaman addini su haΙu su sauya lokacin azumi ya zama kamar lokaci guda da ake Kirsimeti a Ζarshen shekara.
Kalamansa sun haifar da caccaka da zazzafar muhawara a kafofin sada zumunta musamman a Tunisia da sauran Ζasashen Gabas Ta Tsakiya.
Ya kuma sake fitowa a wata tashar Rediyo ta "Mosaic FM" yana kare kalamansa cewa yana da Ζ΄ancin ya bayyana ra'ayinsa tare da Ζin amincewa ya fito ya janye kalamansa da kuma neman afuwar Musulmi kan abin da ya faΙa.
Yawancin waΙanda suka yi tsokaci a kafafen sada zumunta sun caccaki kalaman Al-Sayyari ne, wasunsu sun ce rashin ilimin addini ne ya sa har Ιan fim din ya furta kalaman.
@fbati91 cewa ya yi "Ιan fim na Tunisia Mohamed Al-Siyari kamar ya mayar da addini abin wasa. Jahilci bala'i ne "
Haka ma @saberlarbi ya caccaki Muhammad Al-Siyari kan kiran da ya yi na a dawo yin azumi zuwa watan Disamba.
Wasu daga cikin masu caccakarsa sun ce ya yi kalaman ne kawai "don ya ja hankali don farfaΙo da sunansa saboda rashin aikin yi, kamar yadda Samir Elwafi ya bayyana.
A tsokacinsa Ali Guesmi ya ce "Mohamed al-Siyariya ya fahimci addini amma abin da ya kasa fahimta shi ne yanayi.
A Ιaya Ιangaren kuma wasu sun bayyana rashin jin daΙi kan yadda "ake suka da caccakar Al Siyari kan kalamansa, da kuma rashin tattaunawa ta fahimta da mutuntawa a tattaunawar.
Akram Al Zribi a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook ya nuna cewa ya kamata a yi bincike game da batun ta hanyar hujjoji daga ayoyin Qur'ani, ba wai suka ba da jifar kalamai na zagi da nuna wani ya yi Ιatanci ba.
Al-Siyari Ιan wasan fim ne wanda ya sha fitowa a fina-finan Larabawa musamman masu dogon zango.