TSOHUN DAN WASAN BARCELONA RONALDINHO YA BAYYANA KASA GUDA BIYU DA ZASU IYA DAUKAR KOFIN DUNIYA

Shahararren dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, ​​Ronaldinho, ya zabi Spain da Brazil a matsayin kasashen da ya fi so su lashe gasar cin kofin duniya ta FIFA a shekarar 2022 a Qatar. nairaside.com.ng

A ranar Litinin 21 ga watan Nuwamba ne za a fara gasar cin kofin duniya ta FIFA ta 2022 a filin wasa na Al Thumama lokacin da Senegal za ta fafata da Netherlands a rukunin A, sai kuma Qatar mai masaukin baki da Ecuador a filin wasa na Al Bayt.

Spain tana rukunin E tare da Costa Rica/New Zealand, Jamus da Japan.

Ita kuwa Brazil tana rukunin G ne da Serbia da Switzerland da kuma Kamaru.

Da aka tambaye shi sunan kasar da yafi so ta lashe gasar cin kofin duniya ta 2022, Ronaldinho ya shaida wa World football cewa, “Akwai da yawa da suke da karfi. Kamar tawagar Luis Enrique ta Spain.

“Luis kocin Spain ya kasance abin al’ajabi a ciki da wajen fili, amma ina ganin Brazil ma tana da kyau sosai

Nairaaide.com.ng

Post a Comment

Previous Post Next Post