Wani dan bautar kasa, Khamis Musa Darazo, ya sallama alawus-alawus dinsa na wata-wata ga Jagoran Jam’iyyar APC na kasa kuma mai son tsayawa takarar shugaban a 2023, Asiwaju Bola Tinubu, a matsayin gudunmawarsa ga fadi tashin Tinubu na neman kujerar shugabancin Nijeriya.
Dan bautar kasar ya bayyana cewar yana son alawus dinsa na farko na watan Afrilu ya mika shi ga Tinubu kyauta a matsayin tasa gudunmawar na sayen Fom din nuna sha’awar takarar shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC.
Darazo, wanda a yanzu haka yake aikin yi wa kads hidima a jihar Gombe, ya sanar da wannan matsayar tasa ne a ranar Juma’a lokacin da ke ganawa da manema labarai a Bauchi, ya ce ya mara wa Tinubu baya ne saboda cancantarsa da ya gani da kuma imanin da ya yi na cewa zai iya shawo kan matsalolin da suke addabar kasar Nijeriya da ceto ta daga halin da take ciki a yau.
“Kwata-kwata ma Tinubu bai san da wannan sa’ayin nawa ba, bai taba sani ba, ba mu kuma taba haduwa da shi ba. Kawai ina yin wannan ne saboda tsantsar soyayya da nake mishi