Rahotanni sun ce mayakan sun shiga garin Gaidam din ne da kafa, kafin su kai hari a wata mashaya ta hanyar yi wa mutanen da suka tarar 10 yankan rago. Daga bisani sun karasa zuwa wata makarantar sakandare inda nan ma su ka yanka mutum daya, kuma suka cinna wa makarantar wuta
Wasu daga cikin mutane garin Gaidam sun shaida wa wakilinmu a yankin cewa sun fada tashin hankali, kana kuma an ruwaito cewa jami'an tsaro su bi sawun mayakan a dazukan da ake ganin sun buya.
A baya bayan nan dai kungiyar Boko haram da ISWAP sun kara tsananta kai hare-haren a wasu sassan jihohin Borno da Yobe duk da nasarori da sojojin Najeriya ke ikrarin yi kan mayakan.