- Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga 'yan kasar da su guji mutanen da ke hankoron ganin sun karya doka a kasar.
Wata sanarwa da kakakin shugaban kasar Malam Garba Shehu ya aike wa manema labarai ta ambato Shugaba Buhari yana mai tabbatar wa 'yan kasar cewa ba zai kyale wani ya karya dokokin kasar ba.
''Muna da kasa, muna da albarkatun kasa da kuma mutane. Sai dai ban san dalilin da ya sa wasu ke da niyyar ba da kansu ba wajen lalata Ζasarsu ba," a cewar Buhari yayin buΙe baki da ya yi da gwamnoni da ministoci a Abuja ranar Talata.
Shugaban ya sake jaddada cewa Ζaddamar da amfani da fasahar na'urar tantance masu kaΙa Ζuri'a "ba za ta bari wani ya yi iΖirarin samun miliyoyin Ζuri'u" yayin babban zaΙe na 2023 mai zuwa.

- Copyright: State House
LABARAI DA DUMI-DUMIBuhari na halartar taron APC kan jadawalin zaΙen fid da gwani
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na halartar taron Majalisar Zartarwa na jam'iyyar APC mai mulkin Ζasar da ke gudana yanzu haka.
Ana gudanar da taron ne a otel Ιin Transcop Hilton da ke Abuja karon farko tun bayan da APC ta zaΙi sabbin shugabanninta a watan Maris.
Ana sa ran 'yan majalisar wanda Buhari na Ιaya daga cikinsu, za su daddale jadawalin zaΙukan fid da gwani na jam'iyyar a matakin shugaban Ζasa da kuma na jihohi.
Za mu kawo Ζarin bayani da zarar mun samu...
Tags:
SIYASA
