babbar jarumar kannywood wato safara'u kwanachasa'in takoma rera wakar hausa flim

Tsohuwar jarumar datake taka rawa acikin shirin Kwanacasa’in shiri mai dogon zango na tashar arewa24, wanda ake nunasa duk ranar lahadi da misalin karfe takwas na dare.

Tsohuwar jarumar dai takoma waka, inda tayima kanta wata waka mai taken (Nan gani nan bari kwalelenka) wannan itace wakar da jarumar tayima kanta tareda taimakon wani mawakin hip hop maisuna Mr-442.

Cikin wani faifan bidiyon jarumar wanda ya bayyana inda aka nunota tana tsaye rike da abun magana wanda mawaka suke amfani dashi acikin dakin daukar waka wato (studio) inda a gefe kuma shi dayan mawakin Mr – 442 yana zaune kan kwamfutarshi yana tafiyar da aikin.

MU WAIWAYI RAYUWAR SAFARA’U TA BAYA

Jaruma Safara’u dai tafara taka rawa acikin shirin Kwanacasa’in shiri mai dogon zango kuma shiri mai farin jini wanda mutane suke kallonsa a Tashar arewa24.

Saidai ana tsaka da shirinne dai wani faifan bidiyon jarumar ya bayyana, wanda acikin faifan bidiyon anga tsaraicin jarumar wanda hakan ya tilastawa tashar arewa24 janca jarumar da maye gurbinta da wata sabuwar jaruma.

Wannan yasa aka daina ganin fuskar Safara’u acikin kowani irin fina finan hausa, aka dainajin duriyarta koda kuwa a kafofin sada zumunta ne, saidai kwatsam a jiya saiga faifan bidiyon jarumar tana rerawa kanta waka kamar yadda zakugani.

Kucigabada bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin samun labarai cikin sauki akoda yaushe mungode.

Post a Comment

Previous Post Next Post