Aung San Suu Ky: Kotu ta ɗaure shugabar da ta goyi bayan kisan Musulmai a Myanmar

Wata kotu a Myanmar ta yanke wa babbar jagorar siyasar kasar, Aung San Suu Kyi, hukuncin daurin shekaru biyar a gidan-yari, bisa zargin cin hanci da rashawa.

Shari'ar ta mayar da hankali kan zargin da ake yi wa matar na yin awon-gaba da zinaren da darajarsa ta kai dala dubu dari shida lokacin da tana kan mulki.

Ta yi watsi da zargin da ta bayyana a matsayin shirme.

Alkalin da ya sanar da hukuncin ne jim kadan bayan fara zaman shari'ar da aka dade ana jira.

Wannan dai ita ce shari'a ta farko da aka kammala da gwamnatin mulkin soji ta gabatar tun bayan kwace mulki.

Ba wanan ne karon farko da Suu Kyi wadda ta taba lashe lambar yabo ta Nobel ta taba zaman gida yari ba.

An yi wa Ms Suu Kyi daurin-talala a watan Fabrairun 2021 lokacin da sojoji suka kifar da gwamnatinta da aka zaba.

Wannan hukuncin na nufin za ta yi shekara 11 a gidan-yari, domin kuwa a baya an same ta da laifi kan wasu zarge-zargen.

Ms Suu Kyi - da mambobi da dama na jam'iyyarta - na cikin fiye da mutum 10,000 da sojojin suka kama bayan sun kwace mulki.

A baya ta goyi bayan matakin da sojojin kasar suka dauka na kisan dubban Musulmai 'yan kabilar Rohingya a 2017 lamarin da ya tilasta wa dubban su yin hijira zuwa Bangladesh.

Post a Comment

Previous Post Next Post