ancelotti ya Fadi wata magana ta ban mamaki akan benzema Kuma haka abun yake

Carlo Ancelotti ya amince cewa Real Madrid ta dogara sosai kan tauraron dan wasanta Karim Benzema, wanda ya zura kwallaye uky a wasanni biyu na karshe na gasar zakarun Turai. Nairaside.com.ng ta rahoto.

Kocin dan kasar Italiya ya yi imanin cewa dogaro da dan wasan da ya ke da darajar Benzema alheri ne ga Los Blancos, wadda ke kan gaba wajen ganin ta tsallake zuwa matakin dab da na kusa da na karshe a gasar zakarun Turai bayan ta doke Chelsea da ci 3-1 a wasan farko na wasan kusa da na karshe..

Mun dogara da Benzema, in ji Ancelotti yayin taron manema labarai na ranar Litinin kafin karawar ta biyu da Chelsea.

“Haka abin yake, ba za mu karyata hakan ba. Kuma na yi matukar farin ciki da muka dogara da Karim, gaskiya ne, kuma abu ne mai kyau.

Karim dan wasan gaba ne na zamani kuma yana yin abin da ake bukata na ‘yan wasan gaba. Komai, gami da aikin ceto. Shi ne cikakken wakilcin abin da ya kamata dan wasan gaba ya kasance a wasan kwallon kafa na yau.

Ancelotti ya jaddada cewa ba zai bar Everton zuwa wata kungiya ba a bazarar da ta wuce, amma a karshe ya yanke shawarar rabuwa da Toffees bayan da Real Madrid ta zo ta buga masa kofa.

Ancelotti ya kara da cewa “(Real Madrid) ita ce kungiya daya tilo da na kasa cewa a’a.

“Idan da wata kungiyar ce ta zomin, da na zauna a Everton. Na yi kyau sosai a can. Idan Madrid ta yi farin ciki a karshen kakar wasa, ina tsammanin zan ci gaba da farin ciki, kamar yadda nake a yanzu.”

An tambayi kocin na Real Madrid ko zai so ya horas da ‘yan wasan kasar Italiya kuma ya bayyana cewa yaso ya iya horas da kungiyar a shekarar 2018.

Ancelotti ya ce “A wasu lokuta na yi tunanin zuwa tawagar kasar, amma ina son rayuwar yau da kullun a aikin hotmrarwa, ((rayuwa a kulob))

Na sami damar zuwa Italiya a 2018. saidai na canza tunanin, ba zan je tawagar kasar ba.

“Ba na son yin aiki sau uku a shekara. Idan na gaji da wannan sha’awar ta aikin yau da kullum, zan iya zuwa can. Tabbas ya kasance babban kwarewa don kasancewa cikin ma’aikatan kocin a 1994 World, amma ina son aikin a matakin kulob.

Ancelotti ya kuma jaddada cewa ya kamata Real Madrid ta shirya idan Chelsea ta yanke shawarar sauya salon wasanta bayan ta sha kashi a Stamford Bridge.

“Kowa ya san zai yi wahala, bayan nasara da ci 3-1, in ji Ancelotti.

“Dole ne mu sha wahala kuma mu yi hazaka, tabbas, muna sa ran abokan hamayyar zasuyi kokarinsu don samun nasara.

Za mu gani game da yanayin wasan. Za mu so mu buga wasa iri daya da can. Dole ne mu kasance cikin shiri don komai, don canza salon wasan Chelsea, saboda abin da suka yi a London bai yi m musu aiki da kyau ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post