A cigaba da nishadantar daku jaridar ku ta hausa nairaside.com.ng ta shiga manyan jaridun wasan kwallon kafa na duniya shin meke faruwa?
‘Yan wasa da za su iya barin Man Utd a bazara:
• Paul Pogba
• Jesse Lingard
• Edinson Cavani
• Nemanja Matic
• Juan Mata
• Lee Grant
• Phil Jones
• Alex Telles
• Wan-Bissaka
• Eric Bailly
• Marcus Rashford
• Anthony Martial
( Sun Sport)
– Steven Gerrard ya kasance a Stade VΓ©lodrome a daren jiya don kallon Boubacar Kamara
Kocin Aston Villa yana sha’awar daukar dan wasan na baya idan kwantiraginsa ya kare a bazara.
( RMC Sport)
– Youri Tielemans na shirin barin Leicester City a wannan bazarar, inda Tottenham, Arsenal da Manchester United duk ke zawarcin dan wasan tsakiyar Belgium.
( Sun Sport)
– Kocin AtlΓ©tico de Madrid: Diego Simeone yana sha’awar siyan dan wasan baya William Saliba, mai shekaru 21, bayan aro na Marseille.
(Fichajes)
– Kocin Liverpool FC JΓΌrgen Klopp yana sha’awar siyan dan wasan bayan dama na Aberdeen mai shekaru 18 Calvin Ramsey a matsayin wanda zai marawa Trent Alexander-Arnold baya.
( BILD)
– Kocin Roma JosΓ© Mourinho yana son daukar dan wasan tsakiyar Manchester United Nemanja MatiΔ idan kwantiraginsa ya kare a bazara.
(Tuttomercatoweb)
– Everton na bibiyar halin da dan wasan gaba na kasar Sipaniya Adama Traore yake tare da kungiyar Toffees na shirin yin tayin idan aronsa da Barcelona daga Wolves bai zama na din-din-din ba.
(Football Insider)
Dan wasan gaba na Arsenal Eddie Nketiah yana son buga tamaula akai-akai, tare da Crystal Palace, Leeds United, da West Ham duk suna zawarcinsa. .Sky Sports.
Nairaside.com.ng