Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
Mutumin da ke neman APC ta tsayar da shi takarar shugabancin Najeriya, Adamu Garba, ya koka kan yadda jam'iyyar ta tsawwala kudin sayen fom din takarar.
A tattaunwarsa da BBC Hausa, ya ce a matsayinsa na mutumin da ke yin aiki a kamfanin mai zaman kansa, ba shi da halin sayen fom din takarar shugaban kasa a kan N100m.
Ya ce ya fito takarar shugaban kasa ce domin kawo sauyi a kasar ganin cewa sauyi ba zai samu sosai ba idan mutum bai hau karagar shugabancin kasar ba.
Sai dai ya ce "miliyaan dari ba karamin kudi ba ne; yanzu haka idan mutanen da nake tare da suka ga na tattara naira miliyan dari na je na biya kudin fom, ai kowa zai ce ni barawo ne."