ABIN DA YA SA YAN KORIYA TA KUDU BASA SAMU ISASSHEN BARCI

Rashin samun isasshen barci na da tasiri sosai kan al'ummar kasar Koriya ta Kudu, saboda kasa ce da jama'arta ba su cika samun sukunin yin barci ba.

Ji-Eun ta far fuskantar matsalar rashin yin barci ne bayan da aikin da ta ke yi ya fara hana ta samun damar hutawa.

Akalla t akan yi aiki daga karfe 7 na safe har zuwa 10 na dare, amma a ranakun da aiki ke da yaa, matar mai shekara 29 da haihuwa kan ci gaba da yin aiki har karfe 3 na sanyin safiya.

Shugaban ofishin da take aiki kan kirata a tsakar dare domin y agaya ma ta wasu abubuwan da yake son ta yi na take.

"Na kasance kamar wadda ta manta yadda ake hutawa ma," inji ta.

A gundumar Gangnam ta masu hannu da shuni a birnin Seoul, akwai wani asibiti na musamman mai suna Dream Sleep Clinic, inda Likita Ji-hyeon Lee mai kwarewa kan halayyar dan Adam ke aiki, ta ce ta saba ganin mutanen da kan sha kwayoyin sa barci 20 cikin kowane dare domin kawai su iya runtsawa.

"A hankali barci kan zo wa mutum, amma 'yan Koriya na son bingirewa nan take, saboda haka ne suke shan magani," inji ta.

Sabo da shan magani ya haifar da wata matsala - matsalar dogara ga magani idan za a yi barci, wanda a halin yanzu ya zama annoba a kasar. Babu alkaluman yawan wadanda abin ya shafa amma ana kiyasta cewa akwai 'yan Koriya 100,000 da suka dogara ga shan kwayoyin sa barci kafin su iya yin barcin.

Idan suka kasa yin barci, su kan rika kwankwadar barasa bayan sun sha kwayoyin - halayyar da kan haifar da mummunan hadari ga rayukansu.

Post a Comment

Previous Post Next Post