a p c za ta siyar da form din takarar shugaban kasa kan naira miliyan 100

  1. Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta sanar da sayar da fom ɗin takarar shugaban ƙasa kan naira miliyan 100 a babban zaɓe na 2023 mai zuwa.

    Wani jadawalin gudanar da zaɓukan fid da gwani da jam'iyyar ta fitar bayan taron Majalisar Zartarwarta a yau Laraba ya nuna cewa masu son yin takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin tutar APC za su biya kuɗin na-gani-ina-so naira miliyan 30, sai kuma kuɗin fom naira miliyan 70.

    Kazalika, masu son yin takarar gwamna za su lale naira miliyan 50, yayin da sanatoci za su biya miliyan 20.

    Masu fatan zama 'yan majalisar wakilai za su biya naira miliyan 10. Su kuma 'yan majalisar jiha miliyan biyu.An wallafa a 15:33

  2. Ɗan takarar shugaban ƙasa a APC ya kaɗu da jin farashin fom ɗin takarar

    Adamu Garba

    Mai neman jam'iyyar APC ta tsayar da shi takarar shugaban ƙasa a Najeriya, Adamu Garba, ya kaɗu da jin farashin fom ɗin takararar da jam'iyyarsu ta saka na naira miliyan 100.

    A yau Laraba ne APC ta ce duk mai son ya tsaya takarar shugaban ƙasa sai ya biya kuɗin na-gani-ina-so naira miliyan 30 da kuma kuɗin fom naira miliyan 70.

    Adamu Garba ya bayyana kaɗuwarsa ne a shafinsa na Twitter jim kaɗan bayan sanar da farashin.

    "Miliyan 100 kuɗin fom. Lallai!," kamar yadda ya wallafa.

    Matashin da ke yawan amfani da shafukan zumunta ya kuma nemi 'yan uwansa matasa su fito su "yaƙi jakunkunan kuɗi".

    "Ba zai yiwu mu ci gaba da sayen ofisoshin gwamnati a Najeriya ba, muna buƙatar ƙwararrun shugabanni a (zaɓen) 2023," in ji shi.


Post a Comment

Previous Post Next Post