Lokacin da abin ya faru shi Bappa baya gari domin ya yi tafiya, amma mun gaggauta sanar da jami’an tsaro kan faruwar lamarin.”
Ko a kwanakin baya dai, wasu fusatattun matasa, sun farmaki tawagar Bappan a lokacin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a jihar Neja, inda ya tsallake rijiya da baya, bayan sun faffasa gilasan wasu motocin da ke cikin tawagar.
Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce tana binciken faruwar lamarin tare da alkawalin kubutar da ita cikin koshin lafiya.
Kucigaba da bibiyar shafinmu maisuna Arewajoint domin samun labarai cikin sauki akoda yaushe mungode.