shahk isah Ali fantami Yayi martani Mai zafi wa muhammd gumi akan kashe Debora

TIRKASHI: ASIRIN SHEIKH AHMAD GUMI YA TONU KAN ZAGIN ANNABI S. A. W DA AKAYI A SOKOTO. Sheikh Nasir Ado Musa. T.B.W.

Idan ba a manta ba a cikin satin daya gabata ne wata dalibar kwalejin ilmi ta shehu shagari dake sokoto Wato Deborah tayi batanci ga Annabi Muhammad Salallahu Alaihi wasallam Wanda kusan har yanzu ana cike da jimami gami da tattauna batutuwan dasuka shafi lamarin yayinda jama’a 

da dama kuma ke nuna takacinsu gami da alhininsu musamman bisa ga kama matasan da suka yiwa wannan matashiya babbaka domin turata wajen ubangiji yayi mata hukunci.

Ana cikin wannan kadamin ne katsam sai aka jiyo malamin addinin musuluncin nan Sheik Dr. Ahmed Gumi yana bayyanawa cikin lakcarsa cewar hakika matasan da suka kashe wannan matashiya Deborah sun aikata babban kuskure a addinance, 


inda yakara da cewar bazasu shiga aljannah ba. Wannan magana tashi ta janyo kace nace a ciki da wajen Nigeria musamman a shafukan sada zumunta yayinda mutane da dama suka yi Allah wadai dashi gami da alkawarin daina sauraron 

karatittukansa inda har wani daga cikin malamai wato sheikh Nasir Ado Musa yayi tsokaci kan maganar tashi inda yace tabbas maganar sheikh Dr. Ahmed Gumi kuskure ce, 


kuma daman babu wani dan Adam da ya wuce yinsa a yanzu, amma abunda yake akwai shine idan kayi kuskure aka gyara maka saika karba, bawai kayi isnadi ka nuna taurin kai ba.

MUNA ROKON ALLAH YAKARA DORAMU AKAN DAIDAI AMIN.

Post a Comment

Previous Post Next Post