Matasa a dandalin sada zumunta na ‘Facebook’ sun caccaki Isa Ali Pantami a wani bidiyo da aka gan shi yana jan hankali da nasiha ga masu zaben Primary Election wato Delegate
Matasan dai na yi masa martani da cewa ya zama rikakken munafuki tun da ya shiga gwamnati ya fara amfana, sun kuma kalubalance shi kan shiru da ya yi game da wacce ta yi ‘batanci ga Manzon Allah S.A.W wato Deborah. Kuma dukkanin malaman Allah da Annabi sun fito sun yi magana.
Sun caccaki Malam Garbati cewa gwamnatin Buhari na zaluntar mutane da tsadar rayuwa kuma ‘yan bindiga na shiga kauyuka su kashe gwamman mutane amma tun da ya sami mukami bai kara magana ya janyo hankalin gwamnati ba kamar yadda ya saba, balle kuma ya yi alkunuti yana rusa kuka kamar yadda ya sha yi a mulkin