TUCHEL YA FADAKAR DA YAN WASAN CHELSEA KANCEWAR DOLENE SUJE FILIN REAL MADRID SUDAWO DA NASARA

Mai horas da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa Thomas Tuchel ya fadawa ‘yan wasan sa su tafi birnin Madrid domin su dawo da nasara birnin London a wannan sa NAIRASIDE.COM.NG ta rahoto.

Mai horas da ‘yan wasan na Blues yayi wannan batu ne bayan da kungiyar sa ta fara farfadowa kuma ta doke Southampton daci 6-0 a ranar Asabar a gasar Premier League.

Chelsea dai tayi rashin nasara a hannun Real Madrid daci 3-1 a wasa zagaye na farko da suka fafata ranar Laraba, Bayan sunyi rashin nasara a satin da ya gabata a hannun Brentford daci 4-1.

Anyiwa mai horas war tambaya akan ko nasarar da suka samu akan Brighton zata dawo dasu cikin wasan da zasu fafata da Real Madrid a wannan satin, Tuchel yace: “Ya zama dole a gare mu mu dawo cikin wasan amma yanzu mun farfado ne daga dogon masashsharar da muka fada.

“Ba abu bane mai sauki ma dawo cikin wasan, Kuma ba dole bane komai ya canza, Amma aikin yana wajen mu, Inaji ajiki na zamu iya, Kuma na fadawa ‘yan wasan gaskiya ta.

“Ina ganin yanzu lokaci ne da zamu yunkura muyi abunda ya dace, Domin a yanzu muna da karfi kuma zamu cigaba da kokartawa.

Katura zuwa wani group 👈

Post a Comment

Previous Post Next Post