Bbc hausa ta samo cewa hukumomi a jihar Filato sun tabbatar da aukuwar lamarin, inda kwamishiniyar kula da harkokin mata ta jihar Filato, Rebecca Sambo ta shaida wa BBC Pidgin cewa lamarin ya auku ne a daren ranar 17 ga watan Afrilu.
Ta bayyana cewa magidancin ya farke wa matar sa ciki da misalin ฦarfe biyu na dare, sannan ya cire mata ‘yan hanjinta.
Mercy mai shekaru 25 a duniya, ta mutu bayan an garzaya da ita zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Bingham a Jos, domin a yi mata tiyata.
Hukumar ‘yan sandan Filato ta bayyana cewa tana kan gudanar da bincike dangane da lamarin.
Magidancin da matar tasa Mercy sun kasance tare a ฦarฦashin igiyar aure har na tsawon shekaru 9, sannan sun haifi yara guda biyu a tare.
Dan uwanta ya bayyana cewa cikin tsakar dare makwabta suka ji tana kurma ihu, ko da aka fito domin kawo mata ษauki sai aka tarar da ‘yan hanjin cikinta a hannunta.
Yanzu haka ‘yan sanda na kan farautar magidanci ruwa ajallo wanda tuni tsere. Magidancin yana dukan matar sa duk lokacin da su ka samu ฦaramin saษani. Na samu na ษauki abinda ya faru yau. Musulmi ne, ina tunanin sun samu saษani ne akan abincin Sahur.
Magidancin bai damu da cewa tana ษauke da cikin ษan sa na biyu ba, ya cigaba da dukan ta. Ta yi ta ihu sannan daga bisani ta samu ta gudu zuwa gidan iyayen ta. Gbolagade ya tsere daga gidan sa bayan ‘yan sanda sun bada sanarwar neman sa ruwa a jallo.