Cristiano Ronaldo zai samu kyautar fan 850,000 bayan ya zurawa Manchester United kwallaye uku a ragar Norwich da ci 3-2. Nairaside.com.ng ta rahoto.
A cewar The Sun, Ronaldo ya haifar da wata yarjejeniya da ta shafi kari a kwantiraginsa bayan ya ci kwallaye 21 a kakar wasa ta bana.
Kwantiragin Ronaldo ya hada da kyautar fan 750,000 idan ya ci kwallaye 20 da karin fan 100,000 idan yaci kwallaye uku.
A yanzu Ronaldo zai na karbar fam 100,000 ga duk wata kwallo da ya ci a ragowar kakar wasan bana.
Haka kuma United za ta biya dan wasan da ya fi zura kwallaye a kakar wasa ta bana fam miliyan 1 kuma da alama Ronaldo ya kusa samun wannan kyautar ganin cewa yana gaban abokin karawarsa Bruno Fernandes da kwallaye 12.
Bugu da ฦari, Ronaldo zai karษi kusan fam miliyan 2.75 a jimlar biyansa idan ya sami nasarar kaiwa ga cin kwallaye 30 a kakar wasa ta bana.
Duk da cewa ya sha suka a wasu lokutan tun bayan komawarsa United a bara, Ronaldo na taka rawar gani a lokacin da yake kokarin ganin ya ci gaba da fatan kungiyarsa ta kare a mataki na hudu.
Ronaldo ya zura kwallaye uku a wasan da suka yi da Tottenham a watan da ya gabata, kuma ya sake buga wasan da Norwich a Old Trafford ranar Asabar.
A minti na bakwai Ronaldo ne ya fara zura kwallo a raga, sannan ya ci kwallo ta 2-0 da kai. Norwich ta samu tagomashi inda Kieran Dowell da Teemu Pukki suka farke kwallayen amma Ronaldo ya tabbatar wa United duka maki uku da bugun tazara.
Sakamakon ya sa United ta koma matsayi na biyar da maki uku tsakaninta da Tottenham. Yanzu United za ta kara da Liverpool da Arsenal muhimman wasanni biyu a waje.