Tauraron dan kwallon Manchester United Bruno Fernandes ya tsallake rijiya da baya bayan da ya yi hatsarin mota a safiyar yau, kamar yadda rahotanni suka bayyana. Nairaside.com.ng ta rahoto.
Kungiyar ‘yan jarida ta yi ikirarin cewa dan wasan tsakiya Fernandes, mai shekaru 27, ya fito daga cikin motarsa ba tare da wata matsala ba bayan wani lamari da ya shafi Porsche – kuma ana sa ran zai yi atisaye kamar yadda ya saba a yau..
An ce dukkan bangarorin da hatsarin ya rutsa dasu sun fito ne daga motocinsu ba tare da wata matsala ba.
Mai yiyuwa ne kocin rikon kwarya na United Ralf Rangnick zai ba da bayani kan yanayin dan wasan a taron manema labarai na gabanin wasan da zasu yi.
Hadarin Fernandes na zuwa ne kwana guda gabanin da kungiyarsa ta buga da Liverpool a gasar Premier.
Ya kasance dan wasa mai mahimmanci a kungiyar tun bayan komawarsa daga Sporting Lisbon a watan Janairun 2020, inda ya zura kwallaye 49 a wasanni 120 da ya buga.
A kakar wasa ta bana, ya zura kwallaye tara kuma ya taimaka 14 a wasanni 40.