BABU LAIFI IDAN MUTUM YAYI BIKIN BIRTHDAY BABBAN MALAMI A SAUDIYYA

Wani tsohon mamba a majalisar manyan malaman Saudiyya, Dr. Qais Bin Muhammad Al-Sheikh Mubarak, ya ce babu wani laifi idan Musulmi ya shirya bukukuwa kamar murnar zagayowar ranar haihuwarsa ko kuma 'yan uwansa.

Cikin rahoton da jaridar Saudi Gazette ta ruwaito, shehin malamin ya ฦ™ara da cewa haka abin yake idan mutum ya yi bikin tunawa da wani abu kamar wata nasararsa, ko ta 'ya'yansa, ko samun shaidar karatu ko kammala jami'a.

A cewarsa, abin da kawai ya kamata a lura shi ne halal ne kawai amma babu haramci a kan hakan a cikin Musulunci, yana mai cewa bukukuwan na al'ada ne waษ—anda ba su da alaฦ™a da abin da addinin ya hana.

Al-Mubarak ya ce waษ—annan lamura ba sa cikin ayyukan addini da aka hana Musulmi ฦ™arawa ko rage wani abu daga ciki. Ba kamar faษ—in Annabi SAW ba cewa: "Duk wanda ya ฦ™irฦ™iri wani abu a cikin wannan lamarin namu (Musulunci) da babu shi a cikinsa, ba za a karษ“a ba," a cewrsa.

Malamin ya jaddada cewa babu laifi idan mutum ya yi amfani da lokutan hijirar Annabi a matsayin matashiya ko alฦ™iblar gudanar da ayyuka a rayuwarsu ta yau da kullum.

Post a Comment

Previous Post Next Post