WAYE BROKER*
Kamar yadda nace zamu magana akan Broker, Yana da matukar amfani a harkar forex Trading, Nasan zakuyi Tinanin cewa mu ina zamu samu wadannan kudaden na kasashen Duniya?
To shi Broker yana da duk wadannan Kudade.
Sannan kuma kai tsaye ba zaka iya isa zuwa kasuwar Forex Trading ba, wannan broker din ne dai zai sadaka ka da kasuwa.
Kai a matsayin ka na Individual Person yana da matukar wahala ka samu saduwa da kasuwar Forex kai tsaye, Dan sai ka cika wasu manya manyan sharudai.
Domin kuwa kafin ka samu damar shiga kasuwar forex Trading sai kana da makudan kudade da sukakai Dollar Million Dari (100,000,000), kaga kuwa hakan abu ne mai matukar wahala.
To shi Broker ne zai biya wannan kudin (Dollar Million dari) da kuma wasu sharudai sannan ya shiga kasuwar forex.
Daga baya kuma sai ya dawo ya bude wani business nashi ya ringa amsar kudi a hannun mutane domin suma ya sadasu da wannan kasuwa ta forex, ta Hanyar baka abinda akecewa *Leverage* zamuyi bani akan Leverage a gaba.
*WACE RIBA SHI BROKER ZAI SAMU?*
Wani zai iya tambaya menene ribar su wadannan broker din? Tabbas sunada Riba karku manta nace duk abinda ka siyaa anan kasuwar xaka siyar dashi..kai dai kawai ribarka ita zata dawo maka.
Toh tunda kasuwar bata mutane bace kenan dawa nake kasuwanci? wannan ma wata tambaya ce da wani xai iya yinta.
A Forex akwai abinda muke cewa BID price da kuma ASK price. sune mutanen Forex. Mu dauki BID price. Shi wannan Farashi ne damai Siya ya amince xai siya. Sai Ask price..shikuma farashi ne damai siyarwa ya amince xai siyar.
*MISALI:* Dan uwanka ya turo maka Dolla dubu 10 daga kasar America Tunda a Nigeria kake dole xaka so ka chanja kudinnan xuwa Naira. Sai ka dauki kudin nan ka tafi banki ko dai inda ake canji, domin a chanja maka su xuwa Naira. Da kaje banki sai suka ce maka Farashin ko wacca dala daya daga babban bankin Nigeria misali 350 ne. Sai suka chanja maka kudinka daga daga Dollar Xuwa Naira.
Sai kuma Akai Rashin Sa'a washe gari sai tafiya ta kamaka xuwa America kudinnan da ka chanja a banki ko kwandala baka taba ba. Sai ka dauke su ka tafii banki yanxu kai kaxo da Naira xaka siyi dollar da ita...sai su fada maka A banking su abinda suke siyar da ko wacce dalla 1 shine 515
515 shine Bid price...535 kuma ask price...20 dake tsakani itace ribar banki. A Forex ma abinda yake faruwa kenan tsakanin mu da brokers
Tags:
FOREX