Forex Trading Kasuwa ce Ta Duniya da Ake changing Kudaden Kasashe daban-daban na fadin duniya.
Kasuwar Canji ta Forex Trading Itace Babbar Kasuwa a duniya wanda a kowace Rana ta Duniyar nan Ana Juya Kudade Sama da Trillion 5.6 Dollars $, a kowace Rana.
Wannan Kasuwa Tana Ci ne Tsawon Awa Ashirin da Hudu (24hours) na kowace Rana sau biyar (5) a sati Ranakun aiki daga Litinin zuwa Juma'a.
Duk da dai akwai wasu Indices da Su ku kuma ake Trading nasu Tsawon Kwana bakwai (7days) wato kowace Rana.
Wadannan Indices sun hada da:- Volatility 100, 75, 50, 10. -- Boom 1000 da 500. --- Crash 1000 da 500.
Amma wadannan Indices ba kowane *Broker* ke amma ne dasu ba, mu aje wadannan Indices agefe, sabida mu Broker din da zamuyi aiki dashi baya amfani da Indices, Zamuyi Trading *Currencies* ne kawai.
Nasan wasu zasu Tambaye ni wanene *Broker* so Karku damu, Insha Allah a sannu zamuzo bayani akan *Wanene Broker*.
*MISALI:* Kai ne ko Kece ka shirya Domin barin Nigeria zuwa wata kasar Kamar, Saudia ko America yayi da Kaje Airport zaka bukaci ai ma Canjin kudin kasar ka zuwa na kasar da zakaje, misali zakaje America kaga kenan kana buqatar *American Dollars* domin ba zakai amfani da *Naira* acan ba.
Toh masu chanjin kudi zasu fada ma farashin ko wacca Dollar daya A matsayin Naira kuma haka xasu biya ka.. mu dauki misali duk Dollar daya (1) tana a matsayin Naira 350.
350×100 zai kama 350,000 kaga ba karamin kudi bane. Toh samun Dala 100 a Forex abune mai sauki inhar kasan yadda xakai kasuwancin kuma kana da ilimin abin.
Sai dai A Forex zamu siya (BUY) ne a kasuwar kuma mu siyar (SELL) a kasuwar. lokacin da mukaji cewa kudi Zai kara daraja sai mu siya/BUY. Yana Tashi muna kara cin riba.
Idan kuwa labari muka samu zai rage daraja sai mu siyar/SELL kenan.
Yana kara rage daraja muna cin riba.
Toh ita Forex kasuwace da ake jifan tsuntsu Biyu (2) da dutse daya (1).
*WAYE BROKER*
Kamar yadda nace zamu magana akan Broker, Yana da matukar amfani a harkar forex Trading, Nasan zakuyi Tinanin cewa mu ina zamu samu wadannan kudaden na kasashen Duniya?
To shi Broker yana da duk wadannan Kudade.
Sannan kuma kai tsaye ba zaka iya isa zuwa kasuwar Forex Trading ba, wannan broker din ne dai zai sadaka ka da kasuwa.
Kai a matsayin ka na Individual Person yana da matukar wahala ka samu saduwa da kasuwar Forex kai tsaye, Dan sai ka cika wasu manya manyan sharudai.
Domin kuwa kafin ka samu damar shiga kasuwar forex Trading sai kana da makudan kudade da sukakai Dollar Million Dari (100,000,000), kaga kuwa hakan abu ne mai matukar wahala.
To shi Broker ne zai biya wannan kudin (Dollar Million dari) da kuma wasu sharudai sannan ya shiga kasuwar forex.
Daga baya kuma sai ya dawo ya bude wani business nashi ya ringa amsar kudi a hannun mutane domin suma ya sadasu da wannan kasuwa ta forex, ta Hanyar baka abinda akecewa *Leverage* zamuyi bani akan Leverage a gaba.
*WACE RIBA SHI BROKER ZAI SAMU?*
Wani zai iya tambaya menene ribar su wadannan broker din? Tabbas sunada Riba karku manta nace duk abinda ka siyaa anan kasuwar xaka siyar dashi..kai dai kawai ribarka ita zata dawo maka.
Toh tunda kasuwar bata mutane bace kenan dawa nake kasuwanci? wannan ma wata tambaya ce da wani xai iya yinta.
A Forex akwai abinda muke cewa BID price da kuma ASK price. sune mutanen Forex. Mu dauki BID price. Shi wannan Farashi ne damai Siya ya amince xai siya. Sai Ask price..shikuma farashi ne damai siyarwa ya amince xai siyar.
*MISALI:* Dan uwanka ya turo maka Dolla dubu 10 daga kasar America Tunda a Nigeria kake dole xaka so ka chanja kudinnan xuwa Naira. Sai ka dauki kudin nan ka tafi banki ko dai inda ake canji, domin a chanja maka su xuwa Naira. Da kaje banki sai suka ce maka Farashin ko wacca dala daya daga babban bankin Nigeria misali 520 ne. Sai suka chanja maka kudinka daga daga Dollar Xuwa Naira.
Ku ci gaba da biyomu ta wannan website mai suna www.nairaside.com.ng domin cigaban labarin ko ku Mana magana ta WhatsApp domin kaima ka koya 08127566672
Tags:
FOREX