SIRRIN DA BA KOWA YA SANI BAH A KASUWAR CRYPTO

MAI HAKURI SHINE MAI ARZIKI A CRYPTO


Duk wata harkar neman arziki dole ne mutum sai ya hada da hakuri kafin yaci gajiyarta. To haka abun yake a crypto ma, dolene ka kasance mai hakuri matukar kanason ka ribaci crypto.


Babu mai arziki a crypto sai mai hakuri, sai kuma masu sa'a da ba'a fiye samun irinsu sosai ba, wadanda zaka samu sun siya coin yau gobe zuwa sati daya yayi pumping ya ninninka musu kudinsu.


Indai kakai shekara daya kana crypto na tabbata bazakacemin baka taba yin dana sani ba, ma'ana ka siya coin ka rikeshi tsawon wani lokaci yaqi motsawa saika siyar dashi kuma kaga ba'a fi sati guda ba ya tashi watakila kace idan da baka siyar ba da yanzu kai mai kudi ne. Wasu da yawa sukan alakanta abun da kansu suce sufa komin kyan project din da suka siya baya motsi sai sun siyar.


Shin ka taba tambayar kanka me yake jawo haka?  Matsalar kawai itace rashin hakuri, yawanci mu yan arewa munada gaggawa da kuma tsoron asara. Matukar zaka tsoraci asarar kudinka a crypto, to ina tabbatar maka zakayi ta asara kuwa. Saboda haka zakaji ana cewa. 

Saboda zaka siye coin kaga yana faduwa wancan kuma yana tashi anan zakace zaka siyarda naka kaje ka siya wancan kana siyan wancan din kuma watakila shi kuma ya gama tashinsa faduwa zai komayi kayi ta yawo daga karshe harma ka rasa ina kudin suka nutse.


Kayi iya bincikenka akan coin, idan harka gamsu dashi kayi kokarin ganin kayi holding dinsa na tsawon lokaci musamman a irin wannan lokacin na dip. Duk project din da zaka rikeshi tsawon shekara daya ko biyu indai mai kyau ne zaka sha mamakin irin alheri da zai baka. 

(Invest what you can afford to lose)

Post a Comment

Previous Post Next Post